Matar Aure ta maka Sahibinta a gaban Kotu, ta ce baya bata abinci ya kwamushe kayan ɗakinta ya siyar
- Wata mata ta kai karar sahibinta gaban Alkali, tace baya iya sauke nauyin ciyar da ita, kuma ya barta a gidansu tsawon shekara ɗaya
- Matar ta shaida wa Alkalin Kotun Musulunci a Kaduna cewa Mijin nata ya kuma kwashe kayan ɗakinta ya sayar da su
- Magidancin ya amsa wasu laifukan ya ce yana kaunar matarsa kuma ya miƙa mata dubu guda a gaban kowa a Kotu
Kaduna - Wata matar aure, Bilkisu Ahmed, a ranar Talata ta kai ƙarar maigidanta, Malam Sulaiman, gaban Kotun Shari'ar musulunci dake Kaduna bisa zargin sayar mata da kayan ɗaki.
The Nation ta rahoto cewa matar wacce ke zaune a Anguwar Rigasa Kaduna ta shaida wa alƙali cewa Sahibinta ya sayar da kayan ɗakin biyo bayan gazawarsa wajen samar mata da abinci.

Source: Twitter
A cewar mai shigar ƙara, kusan shekara ɗaya kenan mai gidanta ya gaza sauke nauyin da Allah ya ɗora masa na ciyar da ita.

Kara karanta wannan
Karin Bayani: Tsagin Mala Buni ya kwace ikonsa a Hedkwatar APC, ya faɗi gaskiyar abun da ya faru
A kalamanta tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sama da shekara ɗaya kenan ina zaune tare da iyaye na, ina rokon ya sake ni matuƙar ba zai iya ɗaukar nauyin kula da ni ba.
Shin ya amsa laifinsa?
Da yake martani ga zargin da mai ɗakinsa ta jingina masa, Sulaiman ya musanta aikata wa matarsa ba dai-dai ba.
Sai dai Magidancin bai musanta cewa ya sayar da kayan ɗakin matarsa ba kamar yadda ta yi ikirari tun farko.
A nasa jawabin ya ce:
"Na shiga halin jarabawa ta bangaren samun kuɗi, ba na iya ɗaukar nauyin iyali na. Ina son matata kuma a shirye nake na yi aiki duk wahalarsa wajen biyan bukatunta."
Sulaiman ya kuma damƙa wa matar kudi naira Dubu guda a zauren Kotun tare da alƙawarin nema musu wurin zama ba da jimawa ba
Wane mataki Aƙali ya ɗauka?

Kara karanta wannan
Ka yi murabus yanzun nan ka mika mulki ga Osinbajo, Gwamnan PDP ga shugaba Buhari
Alƙalin Kotun, Mai Sharia Malam Salisu Abubakar-Tureta, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 28 ga watan Maris, inda zasu ba shi ba'a sin sasancin da suka yi.
Alƙalin ya kuma umarci Magidancin ya rinka baiwa matarsa N500 kullum har zuwa lokacin da za'a kawo ƙarshen matsalar.
A wani labarin na daban kuma Budurwa ta danna wa tsohon saurayinta wuka har lahira kan kyautar N3,000 da zasu raba
Dakarun yan sanda sun yi ram da wata matashiyar budurwa bisa zargin halaka tsohon saurayinta kan kudi a Legas.
Matar wacce ta yi dana sanin abin da ta aikata, tace lamarin ya fara ne daga kyautar N3,000 da aka musu su raba.
Asali: Legit.ng