Ma'aikacin Jami'ar Najeriya ya rasu yana tsaka da shakatawa a Swimming Pool
- Wani ma'aikaci a jami'ar UNICAL ya rasa rayuwarsa yayin da yaje Otal shan iska saboda zafin da ake a birnin Kalaba
- Wata majiya ta bayyana cewa da farko an nemi mutumin an rasa amma wajen karfe 2:00 na dare aka ga gawarsa a saman ruwa
- Jami'an yan sanda sun zo sun kama shugaban Otal ɗin da kuma mai tsaron ɗakin siyar da kayan sha da abinci
Calabar, Cross River - Wani ma'aikacin jami'ar Kalaba (UNICAL), Mista Ubong, wanda ke aiki a Ofishin Rijistara ya rasa rayuwarsa a ɗan karamin kwatamin ruwa a Kalaba, babban birnin jahar Cross Riba.
Jaridar Tribune ta rahoto cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na dare a Orange Resort swimming pool dake Lamba 151 kan hanyar MCC, cikin Birnin Kalaba.
Mutane sun tsinci gawar ma'aikacin jami'ar ne bayan ya fita domin shan iska kasancewar yanayin da ake ciki na zafi.
Mista Ubong ɗan shekara 41 a duniya ya bata a Otal ɗin da ya je shaƙatawa, amma daga bisani aka tsinci gawarsa a saman ruwan awanni hudu bayan haka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani majiya da ya nemi a ɓoye bayanansa, ya ce Ma'aikacin ya je shagon siyar da kaya domin siyan abun sha da kayan abinci bayan ya bar gidan da yake zaune.
Mutumin ya ce:
"Ya zo Otal ɗin da nufin shan iska saboda matsanancin zafin da ake fama da shi a Kalaba. A Otal ɗin ya je ya siya kayan sha da abinci, sai kuma ya wuce Swiming Pool ba tare da ya sanar da kowa ba."
"Da misalin karfe 2:00 na dare mai tsaron wurin siyar da kayan sha ya tuna akwai wanda be biya kudinsa ba. Suka cigaba da diba wa har suka ga gawarsa a saman ruwan."
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Majiyar ta ƙara da cewa nan take suka kira yan sanda, waɗan da suka zo suka kama Manajan wurin da kuma mai tsaron shagon kayan sha da abinci.
Duk da har yanzun hukumar yan sanda bata fitar da sanarwa game da lamarin ba, amma mutanen biyu na tsare a hannun su.
A wani labarin na daban kuma Wani mutumi ya halaka babban abokinsa kan Lemun kwalba na N150
Wani mutumi ya yi ajalin babban abokinsa da suka haɗu a wurin mai POS kan lemun kwalba na Naira N150.
Hukumar yan sanda ta jihar Ekiti ta maka shi a gaban Kotun Majistire, kuma tuni alalkali ya aika da shi magarƙama.
Asali: Legit.ng