Rikita-Rikita: Wani mutumi da aka ce ya mutu ya dawo gida bayan shekara 5, Matarsa ta guje shi
- Wasu iyalai yan Najeriya sun shiga rudani bayan dawowar wani ɗan su wanda aka bayyana cewa ya bace kuma ya rasa rayuwarsa
- Mutumin ya ɓata ne yayin tafiya a cikin jirgin ruwa a Kamaru, ya dawo gida bayan shekara 5 amma ya tarad da matarsa ta sake Aure
- Da alama duk kokarinsa na ganin ta dawo gare shi ya ci tura, domin matar ta nuna taji daɗin zama ba zata bar sabon mijinta ba
Bayan shekaru 5 a kasar waje, wani ɗan Najeriya da aka samu labarin ya ɓace ya dawo gida, kuma ya taras matarsa ta guje shi, ta sake sabon aure.
Wani mai amfani da kafar sada zumun ta Tuwita, Victor Israel, da ya rubuta labarin a shafinsa, yace kanin mahaifiyarsa ya fuskanci kalubele kuma ya jefa iyalansu cikin tashin hankali.
A cewar Victor, Kanin mahaifiyarsa ya ɓata a Kamaru cikin wata tafiyar ruwa, bayan duk wani kokarin nemansa na shekaru, sai aka ɗauka ya mutu.
Amma babban abun mamakin shi ne, kwatsam sai ga shi ya dawo gida a cikin watan Janairu na shekarar 2022.
Shin meya faru ya ɓata?
Mutumin ya shaida wa yan uwansa bayan ya dawo cewa kubutar da shi aka yi. Sai dai a halin yanzu ya tarad da matarsa ta yi sabon aure, kuma ba ta da niyyar dawowa gare shi.
Victor ya rubuta cewa:
"Kanin mahaifiyata ya ɓata a Kamaru a tafiyar ruwa. An bayyana cewa ya mutu bayan shekara biyar. Amma abun al'ajabin sai ga shi ya dawo a watan da ya gabata."
"Matsalar ita ce, matarsa ta yi sabon aure kuma ta ce ba zata bar mijinta ba. Kowa ya shiga ruɗani kan lamarin."
Yan Najeriya sun yi martani
@Ellepeter ya ce:
"Ya kubuta kuma bai nemi gida ba bayan haka, matukar ba cikin matsala ya shiga na tsawon lokacin nan ba, zai fi ya koma inda ya fito, ya daina jefa mutane cikin ruɗani."
@gisthaphy ya ce:
"Meyasa bai dawo gida ba bayan ya kubuta lafiya? Dama yana tsammanin mace ta zauna jiransa na tsawon shekaru 5? Ya je ya sake aure kawai ya barta da masoyin ta."
@Vigho_P ya ce:
"Meyasa be dawo ba tun farko? Ya bata da farko wannan ba laifinsa bane kuma bana tunanin matarsa ta yi laifi da ta sake sabon aure. Amma zan so ta koma ɗakinsa."
A wani labarin kuma 'Bama-baman' da yan bindiga suka dasa a kauyen jihar Neja ya tashi da rayukan mutane da yawa
Wasu abubuwan fashe wa sun fashe a kauyen Galadima - Kogo a jihar Neja, lamarin ya yi sanadin rasa rayuka da dama.
Rahoto ya nuna cewa Nakiyoyin sun tashi ne awanni kaɗan bayan harin yan bindiga a kauyuka uku na yankin Shiroro.
Asali: Legit.ng