Wata Sabuwa: Ango ya halarci wurin ɗaura aurensa da tsofaffin kananan kaya, Mutane sun masa rubdugu

Wata Sabuwa: Ango ya halarci wurin ɗaura aurensa da tsofaffin kananan kaya, Mutane sun masa rubdugu

  • Kayan da wani Ango ya sanya a wurin bikin ɗaura aurensa ya fusata mutane yayin da hotunan suka watsu a kafafen sada zumunta
  • Angon wanda ba'a gano bayanansa ba ya halarci wurin sanye da wando Jeans da aka wanke ya fara koɗewa, da kuma ƙaramar riga baƙa
  • Kayan da Angon ya sanya wanda ba'a saba gani ba ya yi hannun riga da kwalliyar da Amarya ta caɓa cikin fararen kaya

Ma'aurata kan yi iyakacin bakin kokarin su wajen tabbatar da sun fita fes-fes ranar ɗaura auren su ko da kuwa haya ne su kan ɗakko na kaya dan kyautata wannan ranar.

Sai dai a wani biki kam ba'a ga irin haka ba tare da wani mutumi da ya Angonce da Amaryarsa.

Angon ya fito cikin wata baƙar riga da kuma wandon Jeans da aka wanke kuma ya fara koɗewa, ko kaɗan kuma babu wata alamar damuwa a fuskarsa.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Ango ya bada mamaki
Wata Sabuwa: Ango ya halarci wurin ɗaura aurensa da tsofaffin kananan kaya, Mutane sun masa rubdugu Hoto: violetprice
Asali: UGC

Amarya ta caɓa ado a ranar bikin

A nata ɓangaren, Amarya yar kimanin shekaru 16 a duniya mai suna, Catherine Nicholson, ta nuna kwarewarta da iya kwalliya yayin da ta yi shigar kece raini a wurin bikin.

A Hotunan da kawarta, Violet Price ta saka a shafin Tik Tok, Catherine, ta yi shigar fararen kaya na Amare wanda babu raini duk wacce ta sanya su.

A Bidiyon da ya biyo bayan hotunan, Violet ta nuna yadda sabbin ma'auratan suka je wurin shakatawa suna wasanni iri-iri, kuma ta ce:

"Babbar ƙawata da ta shiga daga ciki watanni kaɗan baya, ta shaida mun ba zata taɓa faɗawa soyayya da wani ba."

Mutane sun yi wa Angon rubudugu wajen caccakar shigar da ya yi

Nia Louise ta ce:

Kara karanta wannan

Yan bindigan sanye da kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa har lahira

"Wai yanzun kina faɗa mana cewa haka Angon ya yi a shiga a ranar bikinsa cikin karamar riga."

Daisey Rose ta yi martani da:

"Banbancin shigar kayan su a ranar Aure ni kam ba zan iya ɗauka ba sam."

Robz da Kc suka ce:

"Shigar da Angon ya yi a irin wannan rana ya nuna cewa ba dagaske yake ba."

A wani labarin kuma Soyayya ta ɗibi wani Ɗalibin 400-Level ya zauna wa Budurwarsa jarabawa, Jami'a ta yanke hukunci

Wani ɗalibin Najeriya ya rasa damar karatunsa a jami'ar Ilorin saboda ya rubuta wa budurwarsa jarabawa.

Rahoto ya nuna cewa Ɗalibin ya je dakin zana jarabawa domin taimaka wa budurwarsa ta rubuta Kwas ɗin GNS112 amma aka damƙe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262