Bayan shekara 9, Kotu ta datse igiyoyin auren Sadiya Adamu saboda ta cika daukar zafi
- Wata babbar kotu a Jos, babban birnin jahar Filato ta yanke hukuncin raba auren da ya kwashe shekaru 9 saboda ɗaukar zafin matar
- Mijin mai suna, Ifeanyi Nnadili, ya roki kotu ta raba shi da matarsa, Sadiya Adamu, sabida kullum tana cikin fushi da kuma gaba
- Alkalin kotun mai shari'a, Suleiman Lawal, ya umarci ma'auratan biyu kowa ya tafi hanyarsa daban, sun tashi daga mata da miji
Jos, jahar Plateau - Wata babbar kotun Jos, babban birnin jihar Filato, dake zamanta a Kasuwan Nama, ta raba ma'auratan da suka shafe shekaru 9 suna tare da juna.
Daily Trust ta rahoto cewa kotu ta datse igiyoyin auren wata mata mai suna, Sadiya Adamu, da mijinta mai suna, Ifeanyi Nnadili, saboda ɗaukar zafi (wato saurin fushi).
Da yake sanar da hukuncin da Kotu ta yanke, Alkalin kotun mai shari'a Suleiman Lawal, ya amince da bukatar mijin na raba aurensa da matarsa.
Haka nan kuma Alkalin ya umarci ma'auratan biyu da suka shafe shekaru tare da cewa kowa ya kama gabansa, daga ranar su ba miji da mata bane ba.
Meyasa mijin ya shigar da matarsa ƙara a Kotu?
A korafin da ya shigar gaban Kotun dake Jos, Nnadili ya shaida wa Alƙali cewa ba zai iya cigaba da jurewa da ɗaukar yawan fushin matarsa ba, dan haka yana neman a raba auren su.
Magidancin ya ce:
"Ko da yaushe ta na cikin fushi da kuma ɗaukar gaba da ni a matsayina na mijin ta. A ko da yaushe muna cikin faɗa da rikici, ba zaman lafiya."
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ce bisa haka ne mista Nnadili ya roki kotun ta raba auren su kowa ya kama gabansa.
A wani labarin na daban kuma Ayyiriri, An sha shagali yayin da kwamishinan jiha ya biya sadaki, kayan ɗaki, aka ɗaura auren marayu 20
Taimakon maraya a Addinin mu na musulunci ya na da falala mai ɗumbin yawa, musamman a irin yanayin da muke ciki.
Kwamishinan jihar Zamfara ya ɗauki nauyin kayan daki da sauran abubuwan da suka shafi aure, har aka ɗaura auren marayu 20.
Asali: Legit.ng