Mata 3 da suka yi wa maza zarra, suka fita da digirin ‘First Class’ a ABU Zaria a 2020/21
- An samu wasu mata da suke yin zarra a jami’o'i, su na kammala digiri da mafi kyawun sakamako
- Daga ciki akwai wata Zainab Bello wanda ta gama digirinta da makin CGPA 4.85 a jami’ar ABU Zaria
- An samu macen da ta karya tarihin shekaru kusan 40 a jami’ar ta Ahmadu Bello da ke garin Zariya
A ‘yan shekarun nan, mata sun dage a harkar boko kuma su na yin zarra. A wannan rahoto mun tattaro wasu daidaikun matan da suka zama zakaru.
A jerin za a ji labarin Musa Muminah Agaka, Zainab Bello da kuma Malam Asmau Jibril.
1. Zainab Bello
A ranar Juma’a, 28 ga watan Junairu 2022, Mukhtar Maigamo ya bada labarin ‘yaruwarsa, Zainab Bello wanda ta kammala digirinta a harkar lissafi.
Zainab Bello ta gama digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da makin CGPA 4.85. Ba a taba samun wata mace da ta ciri tuta a sashen lissafin ba.
Malam Mukhtar Maigamo ya ce Zainab Bello ta hardace Al-Kur’ani tun ta na shekara 11 a Duniya, sannan duk ajin da ta je, ita ce ta ke zama ta farko.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Asma’u Jibril
Asma’u Jibril ta gama karatunta a sashen ilmin tsirrai a jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Zariya da maki 4.54, ta kammala makarantar ne a zangon 2020/21.
Legit.ng ta samu labari cewa wannan Baiwar Allah ta na da aure, amma bai hana ta yin zarra a aji ba. Sa’a 24 bayan ta yi jarrabawar karshe ne ta haifi yaronta.
3. Musa Muminah Agaka
Wani Usman Isah Musa ya bada labarin Musa Muminah Agaka wanda sunanta ya shiga littafin tarihi bayan fita daga jami’ar ta ABU Zaria da makin CGPA 4.6.
Musa Agaka ce mutumiyar farko da ta samu digirin farko na 'First Class' a cikin shekaru 38 da kafuwar sashen karantar ilmin ‘Dan Adam a wannan jami’ar.
Tsofaffin ma'aikata sun kai ABU kotu
An ji cewa a shekarar 1996 aka kori wasu ma’aikata daga aiki a jami’ar ABU Zaria. Hakan ta sa su ka shiga kotu a 2012, sai kwanan nan ne aka kammala shari'arsu.
Tsofaffin ma’aikatan sun bukaci a biya su hakkokinsu da suke bin jami'ar, kuma sun yi nasara a kotu inda Alkali ya ce lallai CBN su biya ma'aikatan kudinsu N2.5bn.
Asali: Legit.ng