Kamar wasa: Yadda matashi ya sayar da hotunansa na selfie kan kudi N415m

Kamar wasa: Yadda matashi ya sayar da hotunansa na selfie kan kudi N415m

  • Wani dalibi dan kasar Indonesia ya zama hamshakin attajiri kuma ya ja hankalin jama'a a intanet lokacin da ya canza hoto zuwa NFTs
  • SultanAl Ghozali ya sayar da hotunansa na selfie kan kudi naira miliyan 415, wanda hakan ya sa matashin mai shekaru 22 ya zama miloniya nan take
  • Nasarar da ya yi ta girgiza intanet inda mutane da yawa ke ganin hakan abu mafi kyau a intanet yayin da yake murnar nasarar da ya samu

Indonesiya - A zamanin nan, wayoyin tafi da gidanka sun zo da abubuwa masu yawa ga mutane da yawa.

Wani dalibi dan kasar Indonesiya, Sultan Gustaf Al Ghozali, ya shiga wata duniyar fasahar mai sarkakiya, inda ya sayar da hotunansa na selfie a kan kudi naira miliyan 415. Hakan ya sa ya zama miloniya dare daya.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani ma'aikacin majalisar dokoki ya yanki jiki ya fadi matacce

Al-Ghozali ya ci kuɗi
Kamar wasa: Yadda matashi ya sayar hotunansa na selfie kan kudi N455m | nairametrics.com
Asali: UGC

Dalibin mai shekaru 22 na Kimiyyar Kwamfuta ya canza kusan dukkanin hotunansa guda 1,000 zuwa fasahar kadarar crypto ta NFTs.

Tsawon lokacin hotunan

Rahoton Nairametrics ya ce dalibin ya dauki hotunan da kansa ne na tsawon shekaru biyar tsakanin shekaru 18 zuwa 22 a matsayin abin tunawa da kuma yadda ya waiwayi tafiyarsa ta kammala karatunsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya canza hotunan zuwa NFTs kuma ya loda su zuwa kafar dillanci ta OpenSea a watan Disambar bara.

Yawancin Hotunan Al Ghozali ya dauke su ne a lokacin da yake zaune a gaban kwamfutarsa sannan daga baya ya sauya su zuwa NFT kuma ya kayyade musu farashin N1,123 kowanne.

Sauyin da ya sauya rayuwarsa

Kimanin 933 NFTs na hotunan selfie dalibin ya loda a kafar intanet, tare da masu mallaka 489.

Tarin hotunan dai sun kai ga farashin 333ETH, a kan farashin kudi kuwa, kowane ETH ya Kai darajar N1, 379, 875, wanda ya kawo jimlar zuwa N459,498,475, kamar yadda Legit.ng Hausa ta gano a manhajar Binance.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Harkallar tasa ta girgiza Twitter tare da masoya masu nuna goyon baya da yawa da kuma masu sake yada labarin Al-Ghozali.

A wani labarin, a makon nan ne kamfanin BUA Foods Plc da Alhaji Abdul Samad Rabiu ya mallaka ya samu damar saida hannun jarinsa ga masu sha’awa a Najeriya.

Wani rahoto da Billionaires Africa a fitar ya nuna cewa a sakamakon sa hannun jarin kamfanin BUA da aka yi a kasuwa, dukiyar Abdul Samad Rabiu ta nunku.

Daga Dala biliyan 5.3 a kwanaki, ana maganar arzikin Rabiu ya haura Dala biliyan 7.2 yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.