Bayan mutuwarsa, wani mutumi ya bada labarin alherin da Bashir Tofa ya yi masa a 1991

Bayan mutuwarsa, wani mutumi ya bada labarin alherin da Bashir Tofa ya yi masa a 1991

  • Sulaiman Uba Gaya ya yi rubutun ta’aziyyar rashin dattijon Arewa, Alhaji Bashir Othman Tofa
  • Alhaji Bashir Othman Tofa ya taimakawa Sulaiman Gaya da kyautar N10000 da zai yi aure a 1991
  • A wancan lokacin kudi su na da daraja, shi kuma Gaya matashi ne wanda ya shiga harkar jarida

Sulaiman Uba Gaya, wani babban ‘dan jarida a Najeriya, ya bada labarin alherin da Alhaji Bashir Othman Tofa ya yi masa shekaru talatin da suka wuce.

A wani rubutun ta’aziyya da ya yi a Sun, Sulaiman Uba Gaya ya tuno yadda tsohuwar kyautar da Bashir Othman Tofa ya taba yi masa da ta taimake shi.

Wannan mutumi ya hadu da Alhaji Tofa ne a lokacin ya na gwauro, ya fara aikin jarida a jihar Kano.

Sulaiman Gaya yace a lokacin da zai gayyaci manyan mutane zuwa auren na sa, sai ya sa sunan Alhaji Bashir Tofa a gaba, ya aika masa goron gayyata.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

Tofa ya kira shi har ofis

Abin da bai yi tunani ba ya faru, Gaya ya ce sai kurum ya ji ana nemansa a ofishin Marigayin, da zuwansa ya damka masa kyautar N10000 na hidimar biki.

Bashir Tofa
Marigayi Bashir Othman Tofa Hoto: @bashir.tofa
Asali: Facebook

Kamar yadda ya yi bayani a jaridar, Sulaiman Gaya ya ce N10, 000 a wancan lokacin (Dala $1 ta na kusan N10), tamkar miliyoyi ce a zamanin da ake ciki a yau.

“Ana gobe daurin aure, Tofa ya kira ni gidansa da ke kusa da gidan mahaifina, ya yi mani bayani cewa uzuri ya taso masa zuwa kasar waje washegari.”
“Hakan ya sa ba zai iya zuwa bikin ba, amma ya yi alkawarin turo wadanda za su wakilce shi. Ya cika alkawarinsa, ya turo manyan manajojinsa uku”

Kara karanta wannan

Addini, rashin lafiya, da matsaloli 5 da Tinubu zai fuskanta a neman Shugaban Najeriya

Sadakin auren mata 10

A wancan lokaci N1, 000 ne mafi tsadar sadakin aure da ake biya a fadin kasar Kano inji Gaya. Da wannan kudi ya auri sahibarsa, Maijidda Adamu Gezawa.

Har gobe kuwa Alhaji Gaya yana tare da Hajiya Maijidda Gezawa, da ‘ya ‘yansu shida da yanzu uku sun kammala karatun jami’a, su na neman na kansu.

Da yake marubucin ba ya mantawa da alheri, ya ce ya na ganin cewa wannan gagarumar kyauta da aka ba shi ta taimaka wajen rike aurensa har zuwa yanzu.

Tofa ya rasu

Idan za ku tuna, a ranar 3 ga watan Junairu, 2022, aka samu labarin rasuwar dattijon Arewa, Alhaji Bashir Othman Tofa bayan ya yi a fama da rashin lafiya.

Da mu ka kawo tarihinsa, kun ji cewa tsakanin shekarar 1970 zuwa 1973, Tofa ya na Birtaniya, inda ya yi karatu a City of London College da ke birnin Landan.

Kara karanta wannan

Wayyo: Mai imani ya ci karo da jakar kudi, bai tafi da komai ba sai N1800 na auno masara

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng