‘Yan Sanda sun yi ram da barawon da ya addabi jama'a, ya sace wayoyin salulan mutane 200
- Rundunar ‘yan sanda a jihar Yobe ta kama wani wanda ya gawurta wurin satar wayoyin mutane
- Jami’an tsaro sun dade su na neman wannan mutumi da ake zargin ya saci wayoyi sama da 200
- ASP Dungus Abdulkarim yace Dakarun Crack Squad Unit sun cafke Usman Ali a Nayinawa Sallake
Yobe - Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun kama wani ‘dan shekara 35, Usman Ali da zargin satar wayoyi da sauran dukiyoyin mutane a garin Damaturu.
Daily Trust tace ana zargin Mista Usman Ali da satar wayoyin salula fiye da 200. Daga cikin wayoyin da ya dauke akwai wanda ya saida a kan N800.
NAN tace Mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sanda na jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar
Da yake magana a ranar 8 ga watan Junairu, 2022, Abdulkarim yace ‘yan sanda sun yi ram da wanda ake zargi ne unguwar Nayinawa Sallake, Damaturu.
Kokarin Crack Squad Unit
“A ranar 7 ga watan Junairu, 2022 da kimanin karfe 06:00 dakarun ‘yan sanda na Crack Squad Unit suka samu korafi daga Mai garin yankin Marfa-Kallam.”
“An kawo kara cewa an shiga gidaje har hudu, an sace dukiyoyin mutane a cikin dare guda.”
“Wanda ake tuhuma ya kware wajen burmawa gidajen mutane cikin dare ya dauke abubuwan da ya ci karo da su; wayoyin salula, talabijin, kufi da kayan ado.”
- ASP Dungus Abdulkarim
A jawabin na sa, ASP Dungus Abdulkarim yace Ali ya saba zama wajen mai shayi da masu tuyar indomie domin lura da shiga da ficen mutane a Marfa-Kallam.
“Idan gari ya yi duhu da yamma, sai su labe a wasu wurare, su fito cikin tsakar dare domin su yi aika-aikansu.”
“Sun saba yin barnar ne da kimanin karfe 2:00 zuwa 3:00 na dare, bayan sun shiga gidajen mutane ta kofa ko taga.”
AA Zaura zai raba N200m
Abdulsalam Abdulkarim Zaura, mai neman zama gwamnan jihar Kano a zaben 2023 ya yi alkawarin zai kashe N200m a kan yaran Kano da suke karatu.
Duk wani dalibi daga Kano da yake karatu a daya daga cikin manyan makarantun gwamnatin kasar nan zai iya tashi da gudumuwar N20, 000 a shekarar bana.
Asali: Legit.ng