Jigon gwamnati ya bayyana yadda kyankyaso mai rai ya zauna a kunnensa na tsawon watanni

Jigon gwamnati ya bayyana yadda kyankyaso mai rai ya zauna a kunnensa na tsawon watanni

  • Samuel Ike, sabon sakataren din-din-din na ma’aikatar kasuwanci ta jihar Anambra, ya godewa Allah da irin alherin da ya masa
  • Ike ya yi tsokaci kan yadda Allah ya kubutar da shi daga hauka wasu shekaru baya kafin nadin na sa a matsayin sakataren din-din-din
  • Da yake magana a jihar a ranar Lahadi, bayan kammala hidimar godiya, Ike ya ce wani kyankyanso mai rai ya zauna a kunnensa na tsawon watanni

Sabon sakataren din-din-din na ma’aikatar ciniki da kasuwanci a Anambra, Samuel Ike, ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya ceci rayuwarsa ta hanyar sauko masa da mu’ujiza.

Ike wanda ya yi magana a cocin St. James Anglican a hidimar godiya a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba, kan ikon Allah, ya ba da labarin yadda wani kwaro, kyankyaso ya kutsa cikin kunnensa ya zauna na tsawon watanni kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: 'Yan bindiga sun sace yayana, sun kashe dan direban gidanmu

Sakataren din-din-din, Samuel Ike
Jigon gwamnati ya bayyana yadda kyankyaso mai rai ya zauna a kunnensa na tsawon watanni | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Tribune ya kara da cewa sabon sakarataren na din-din-din ya ce wani likita ya shaida masa cewa zai haukace idan da kwaron ya shiga cikin kwakwalwarsa.

Ike ya ce daga karshe an fito da kyankyanson daga kunnensa sannan aka kashe shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

“Ina so in gode masa domin in ba dan shi ba, da na mutu tuni.
“Lokacin da nake tuki wata rana, na ji wani abu yana motsi a kunnena. Wani matsakaicin kyankyaso ne. Ban san yadda ya shiga kunnena ba.
“Likita ya ce da ni da na zauce da a ce ya yi nasarar shiga kwakwalwata. Aka fitar da shi da ransa muka kashe shi.”

Bidiyon matashi na tura wa 'yan NEPA karnuka yayin da suka zo yanke wuta

A wani labarin, wani faifan bidiyo na bidiyo ya nuna wani matashi da karnuka biyu yayin da ya tsare su daga tsorata jami'an NEPA.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

Kafar Instagram ta @Instablog9ja da ta sake yada faifan bidiyon ta ce matashin ya yi amfani da karnuka wajen hana wasu jami’an NEPA gudanar da aikinsu.

A cikin faifan bidiyon, an ga karnukan sun yi kamar sun shirya tsaf don farmakan jami'an. Bayan mutumin kuwa, an ga wani tsani jingine a jikin pole din wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.