Kabiru Alhasan: Mai hannu daya mai yin sana'ar faskaren itace domin ya rayu a Duniya
- Kabiru Alhassan wani mutum ne da yake yin faskare a Kano, abin mamakin bai da hannu daya
- Alhassan yace tun yana karami ya fara yin wannan sana’a, kuma a haka yayi aure ya samu iyali
- Ya ce ko da hannu daya gare shi, amma sai a kira shi ya yi aikin da masu hannuwa ba za su iya ba
Kano - Kabiru Alhasan, wani Bawan Allah da ya gamu da larura ta rashin hannu guda, ma’ana yana aiki ne da hannu daya ya nuna baiwar da Allah ya yi masa.
BBC Pidgin tayi hira da Kabiru Alhasan, inda ya bayyana cewa yana faskare itace duk da ya rasa hannunsa daya a shekarun baya, a lokacin da yake karamin yaro.
Shekaru 22 da suka shude Alhassan ya je kauye, inda ya fado daga wata bishiya, daga nan ya karye. Sai aka kai shi wajen mai dauri na gargajiya domin ya gyara.
Ba a dace da dauri ba, hannun Alhassan ya fara rubewa don haka aka tafi asibiti aka datse shi. A haka ya zama mai hannu daya, amma bai hana shi neman abinci ba.
Alhassan yace ya dade yana sana’ar faskare, kuma ya kan aikin yi da masu hannuwa biyu ba za su iya ba. Wannan mutumi yace duk da haka bai shan maganin karfi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Sunana Kabiru Alhassan, ina amfani da hannu daya ne wajen faskara itace. Kamar shekaru 20 da suka wuce mu na zaune tare da abokaina sai motar ita ce ta zo."
“Aka sauke itace a gaban gida, sai mu ka dauki gatari kamar wasa, mu ka fara faskare. Sai aka fara biyanmu kudi. Sannu a hankali, a haka na fara wannan sana’a.”
Kabiru Alhasan ba ya tsoron kowane irin itace
“Ina iya faskara kowane irin itace, duk wanda ya gagari mutane sai a kira ni domin in sara shi. – Alhasan.
“Sai a kira ni in yi aikin da masu hannuwa biyu ba za su iya ba, idan na zo sai in faskara su.”
“Wallahi babu abin da na ke sha, karfi na daga Allah ne. Duk lokacin da na gama aiki, sai in tafi gida, in ci abinci, in yi wanka, in kwanta in huta.” – Alhasan.
Wannan magidanci ya shaidawa BBC, da haka ya yi aure, har ya haifi ‘ya ‘ya hudu. Ranar da ba zai manta ba shi ne lokacin da ya yi aikin da ya gagari mutane biyar.
'Yan Bokon asali
A makon nan ku ja ji cewa wani ‘Dan Bokon da ya halarci Jami’o’i 6, ya yi karatun Digiri sama da 5 ya kammala karatun digirinsa na PhD a fannin shari'a a jami'ar Ibadan.
'Ɗan iskan' ajinmu a sakandare ya zama matuƙin jirgin sama, mu masu kamun kai kuma har yau ba mu da komai
Dr. Temitayo Bello ya yi digirin B.Sc, LL.M, MSc, Masters, PHD a fannin tattalin arziki, shari'a, ilmin komfuta, aikin banki, huldatayyar kasashen Duniya a jami'o'i.
Asali: Legit.ng