Yar kasuwa ta damka wa kwastoma wallet din da ta mance a shagonta bayan wata uku, Yan Najeriya sun yi martani
- Wata yar kasuwa ta nuna asalin amana yayin da ta aje karamar jakar aje kudi (Walllet) da kwastomanta ta manta
- Saboda rashin haɗuwa da mai ita, ta cigaba da ajiyar wallet ɗin watanni uku, har sanda me ita tazo siyayya wurinta
- Hoton jakar ya nuna yadda kuɗaɗen dake ciki suka yi ƙura, yayin da mutane suka fara yabo gareta bisa wannan amana
Wata mata yar kasuwa ta sha yabo daga bakin mutane bisa nuna gaskiya da rikon amana na maida wa kwastomanta jakar kudi.
Awodiye Funke, ta bayyana a shafinta na dandalin Facebook, yadda wata mai suna Mama Funke ta manta karamar jakar kudinta wata uku da suka wuce, kuma jakar na ɗauke da kudi da wasu abubuwa masu amfani.
Ta maida mata jakar ta
A ranar Laraba 8 ga watan Disamba, matar da ta yi siyayya a wurinta ta tambaye ta ko da taba mance wani abu lokaci mai tsawo da ya wuce.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da Mama Funke ta faɗa mata, "Eh," matar ta bayyana mata cewa akwai wata karamar jakar zuba kudi tana tsammanin na ta ne.
Yar kasuwan ta kara da cewa ta so maido mata da abinta amma babu abinda za'a tuntube ta a ciki.
Kuɗaɗen ciki sun yi kura
Abin ban mamakin shine matar ba ta taɓa komai daga cikin wallet ɗin ba tsawon watanni uku, kuɗaɗen ciki har sun yi kura.
Awodiye tace duk da mutane ka iya tunanin ta maida wa mai jakar abinta ne saboda kudin ciki basu da yawa, amma abinda ta yi ya kara nuna cewa akwai mutane masu gaskiya a ƙasar nan.
Legit.ng Hausa ta tatara muku wasu daga cikin martanin mutane game da lamarin.
Albert Otto yace:
"Awodiye Funke har yanzun akwai sauran mutane masu gaskiya kamar yadda kika faɗa."
Beauty Oduali-Olusakin tace:
"Inji wa? Wannan kudin zasu iya girka lafiyayyan abinci fa."
Lizi Ben-Iheanacho yace:
"Eh tabbas kuwa, har yanzun akwai mutane masu gaskiya da rikon amana a cikin mu."
Adeyimi Adebiyi yace:
"Kwarai kuwa, har yanzun akwai mutane masu kyawawan dabi'u na ɗaukar darasi."
Francis Eniola Omole yace:
"Eh kam, har yanzun akwai mutane masu rikon amana a ƙasa."
Adeosun Adeshina Faruq tace:
"Wanna abun a yaba mata ne."
A wani labarin na daban kuma Mutane sun yi gudun mutuwa yayin da wata kotu ta rushe ana tsaka da zaman Shari'a
Mutane sun yi gudun tsira da rayuwarsu yayin da rufin ginin wata kotu ya fara rushewa ana tsaka da zaman shari'a.
Rahotanni sun bayyana cewa lauyoyi, ma'aikatan kotu da waɗan da ake tuhuma sun yi kokarin fita domin tsira.
Asali: Legit.ng