Abun Tausayi: Yadda wata mahaifiya ta sadaukar da rayuwarta domin ɗanta ya tsira

Abun Tausayi: Yadda wata mahaifiya ta sadaukar da rayuwarta domin ɗanta ya tsira

  • Wata mata ta sadaukar da jikinta a kokarinta na kare yaron ta daga kifewar wani gini a birnin Istanbul na kasar Turkiyya
  • Rahotanni sun bayyana cewa matar ta saka jikinta a saman ɗan yayin da ta fahimci ginin na gab da rushe wa saboda mamakon ruwan sama
  • Shaidan da abin ya faru a kan idonsa yace yanzu haka ɗan na gadon asibiti, yayin da ita kuma mahaifiyarsa ta mutu nan take

Wata mata ta rasa rayuwarta yayin da ta yi kokarin kare ɗan da ta haifa daga rushewar wani gini da suke ciki.

Daily Nigerian ta rahoto cewa ginin ya fara kokarin kifewa ne da rushe wa lokacin da ake wani mamakon ruwan sama a Istanbul, babban birnin Turkiyya.

Gini mai.kifewa
Abun Tausayi: Yadda wata mahaifiya ta sadaukar da rayuwarta domin ɗanta ya tsira Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Rahotanni daga kafafen watsa labarai na ƙasar Turkiyya, sun nuna cewa ginin ya rufta kan mahaifiyar da kuma ɗanta, har yarufe su baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

Yayin da aka kawo musu agaji, matar ta mutu nan take a gurin da abun ya faru, yayin da a halin yanzun yaron ke kwance a Asibiti yana samun kulawar lafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda matar ta ceci ɗan ta

Wani shaida da abun ya faru a gabansa, ya bayyana yadda matar ta yi kokarin tura kanta domin kada ginin ya hallaka yaron.

A cewarsa, lokacin da matar ta fahimci ginin da suke ciki na shirin ruftawa kansu, sai ta saka jikinta a saman ɗan domin ta kare shi daga cutuwa idan ginin ya kife.

Rahotanni sun bayyana cewa a wannan rana mamakon ruwan ya yi sanadiyyar lalata dukiyoyi da gidaje da dama a Istanbul.

Kazalika an samu rahotannin jin raunuka da dama daga sassa daban-daban na kasar Turkiyya baki ɗaya.

A wani labarin na daban kuma Mutuwa rigar kowa, wani Dan majalisar dokoki a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Kara karanta wannan

Wata mata ta tashi da sama da Naira miliyan 5 daga ajiya sannu a hankali a cikin asusu

Mamba a majalisar dokokin jihar Filato, Henry Longs, ya rigamu gidan gaskiya da yammacin ranar Lahadi da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa Longs, wanda ke wakiltar mazaɓar Pankshin ta kudu ya mutu ne bayan an masa tiyata a kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262