Kungiyar Matasan Arewa ta bada shawarar yadda za a shawo kan matsalolin da ake fama da su
- Society for Arewa Development ta yi zama domin murnar samun ‘yancin kai
- Kungiyar ta tattauna a kan halin da yankin Arewacin Najeriya yake ciki a yau
- A karshen zaman, kungiyar ta fitar da shawarwarin da take so ayi aiki da su
Kaduna - Kungiyar Society for Arewa Development (SOFAD) mai kishin yankin Arewacin Najeriya, ta yi kira ga shugabannin yankin da su tashi-tsaye.
Society for Arewa Development ta yi wani taro domin bikin samun ‘yancin kai a garin Zaria, Kaduna, inda ta tattauna a kan matsalolin yankin na Arewa.
Legit.ng Hausa ta samu zuwa wajen wannan taro da ya gudana a ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba, 2021, wanda ya samu halartar matasa masu kishin yankinsu.
Sahelian Times tace an yi wa zaman da taken “Fathering the Orphaned Arewa Towards Nigeria’s Development”.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Matsayar da aka cin ma a zaman “Fathering the Orphaned Arewa”
Kungiyar SOFAD ta fitar da matsaya bayan wannan taro, inda ta bada wasu shawarwari da za su zama mafita wajen ceto Arewacin Najeriya daga cikin kangi.
Ya kamata Arewacin Najeriya ya yi amfani da baiwar arzikin da Ubangiji ya yi masa ta yadda za a yi amfani da kudin-shiga wajen gina abubuwan more rayuwa.
Yankin Arewacin Najeriya ya dage wajen harkar noma na zamani, a kawo tsare-tsaren da za su sa a rage dogara da arzikin man fetur da shigo da kaya daga ketare
Har ila yau, an cin ma matsaya cewa ya zama dole jihohin Arewacin Najeriya su shigo da wasu manufofin da su taimaka wajen bunkasa kasuwanci a yankin.
Kungiyar ta koka kan yadda ake fama da miliyoyin yara da su zuwa makaranta a yankin, ta bada shawarar ayi wa Almajiranci kwaskwarima, maimako soke tsarin.
A takardar da shugaban kungiyar, Sahabi Sufyan, ya sa wa hannu, ya yi kira ga shugabanni su kira taro na musamman da nufin a kawo karshen matsalar tsaro.
Luguden wuta a jejin Birnin Gwari
Hedikwatar tsaro ta kasa ta bada albishir cewa ta aika ‘Yan bindiga rututu zuwa barzahu a sakamakon wasu hare-hare da ta kai a yankunan Sokoto da Kaduna.
Jami’an tsaro sun kashe miyagun ‘yan bindiga sama da 40 tsakanin farkon Oktoba zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng