Latest
'Yan majalisa sun ba Tinubu gudunmawar N705m domin a ragewa talakawa radadin wahalar tattalin arziki, sun ce sun cika alkawarin ba da rabin albashinsu ga mabukata.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shahararren malamin cocin katolika na Sakkwato, Bishof Mathewa Kuka a matsayin shugaban majalir gudanar na Jami'ar Kachia.
Yan takara 200 da suka fafata a zaben kananan hukumomin jihar Kaduna tare da magoya bayansu akalla 10000 sun tattara kayansu daga NNPP, sun koma SDP.
Gwamna Abba Yusuf ya naɗa Ibrahim Adamu Kwamishinan Raya Gidaje na Kano, yana mai buƙatar ya tunkari matsalar gidaje, musamman ga ma’aikatan gwamnati.
Jam'iyyar APC ta ƙasa ta soki tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai kan sauya sheka zuwa SDP, ta ce sukar da ya yi wa gwamnatin Tinubu ba gaskiya bane.
Rundunar ‘yan sanda ta Rivers ta musanta cewa an kai hari kan gidan Nyesom Wike, tana mai cewa rahoton ba gaskiya ba ne, don haka jama’a su yi watsi da shi.
Jam'iyyar APC ta ce babu adalci a ce shugabancin Majalisar dokokin jihar Filato na hannun YPP duk da ita ke da mafi rinjayen mambobi 22 cikin 24.
An samu barkewar sabon rikici tsakanin masu bautar gargajiya da matasan Musulmi a jihar Plateau. Mutane da dama sun jikkata yayin da aka kona wuraren bauta.
Gwamnatin Kano ta bukaci ma’aikatan jihar da su tantance albashinsu na Maris, kafin ta fara biya, tana mai cewa za a biya kafin Sallah don su samu walwala.
Masu zafi
Samu kari