Latest
A labarin nan, za a ji cewa wani Shehin Malamin addinin Musulunci, Sheikh Aliyu Muhammad Sani ya ce Iran da Isra'ila na kokarin raunata kasashen Larabawa.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya zargi duka ƙasashen Isra'ila da Iran da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta, yana mai ɗora babban laifi kan ƙasar Yahudawa.
Farashin mai ya faɗi da kusan 5% bayan Isra'ila ta amince da tsagaita wuta da Iran. Kasuwannin duniya sun farfaɗo. Brent ya dawo $69, yayin da WTI ya koma $66.14.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi wa Bola Tinubu alkawarin kuri'a miliyan 2.5 a zaben 2027. Gwamnan ya ce Tinubu na ayyuka sosai a jihar Edo.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Alex, wani ɗan kasuwa daga ƙasar Belarus a matsayin abokin karatunsa a jami'ar Chicago da ke ƙasar Amurka.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa babu wanda zai sake zaben Bola Tinubu a babban zaben 2027 mai zuwa.
Kasar Isra'ila ta ce za ta cigaba da kai hare hare zuwa Iran bayan cimma yarjejeniya a tsakaninsu. Isra'ila ta ce Iran ta karya yarjejeniya amma ta musa.
Tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran ta rushe bayan harba makamai masu linzami. Netanyahu ya tabbatar da cewa Isra'ila ta kai hari, kuma ta cimma burin yaƙi.
Wasu kungiyoyi a Arewa maso Gabas sun saba da juna kan wanda ya kamata a dauka a madadin Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa a zaben 2027.
Masu zafi
Samu kari