Latest
Kowane mai rai watarana zai dandani mutuwa, Allah ya yi wa shugaban jami'ar Achievers, Farfesa Samuel Aje rasuwa bayan ya tafi hutun bikin kirsimeti Legas.
Foluke Abosede Ntukdem, tsohuwar sarauniyar kyau ta Najeriya ta riga mu gidan gaskiya. Ta rasu a gidanta Legas a cikin barcinta kamar yadda danta ya tabbatar.
Abokin takarar Atiku a zaben shugaban ƙasan 2023 kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce da zaran PDP ta koma kan madafun iko, yunwa ta kare a kasa.
Hukumar kashe gobara ta jihar Legas da Ogun sun tabbatar da tashin wata gobarar cikin dare a fitacciyar kasuwar Ajimula dake tsakanin iyakokin Ogun da Legas.
Wata soja da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan ta'adda bayan da sojoji suka yi kokarin kwato ba. An bayyana yadda wasu 'yan bindiga suka sace budurwar a Kudu.
Wani bidiyon ban dariya da ke yawo a manhajar TikTok ya nuno wata matar aure tana sharban kuka wiwi bayan mijinta ya bukaci lallai ta wanke kayanta masu datti.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya gana da Sufetan yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba, a hedkwatar Abuja kan kisan da aka yi wa Lauya a jaharsa.
Wata budurwa 'yar Arewa ta ba da mamaki yayin da aka ga tana buga kwallo kamar wata kwararriyar da ta dade tana wasa. Jama'a sun shiga mamakin wannan budurwa.
Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda, PSC, ta amince da dakatar da ‘Dan sandan da ake zargi da bindige lauya Bolanle Raheem a ranar Kirsimeti a jiharr Legas.
Masu zafi
Samu kari