Latest
Shugaban cocin RCCG a Najeriya, Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa su na tare da kasar Isra'ila yayin da ake ci gaba da gwabza mummunan fada a yankin.
Ministan kudin Najeriya, Wale Edun ya zama shugaban kungiyar gwamnonin Afrika a bankin duniya, sai yanzu kujerar ta iya isowa kan ‘dan Najeriya a shekaru 60.
Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Najeriya, ACP Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa an kama wanda ya sace daliban FGC Yauri da wasu miyagun masu satar mutane.
Hukumar EFCC ta yi bayanin irin cigaban da ake samu a kokarin da ta ke yi na cafke barayi. Tsofaffin gwamnoni da ministoci da kuma tsohon Akanta Janar ake bincike.
Jiragen yaƙin rundunar sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta kan miyagun ƴan bindiga a jihar Zamfara. Harin ya ƙona ƴan bindiga sama da 100.
A halin yanzu ana fama da tashin farashin kaya da tsadar dala a Najeriya. IMF sun tsoma baki ganin lissafi ya na neman kwacewa sabon Shugaban kasa.
Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Ƙashim Shettima da wasu gwamnonin jam'iyyar APC 14 sun sauka a jihar Imo yayin da APC zata kaddamar da kamfe.
David Yusuf, wani malamin makarantar sakandiren mata a babban birnin tarayya Abuja ya wati gari a gidan yari bisa tuhumar lakaɗa wa daibarsa dukan tsiya.
Kamfanin simintin Dangote ya fito fili ya yi magana kan batun da ke yawo mai cewa ya shirya rage farashin kowane buhun siminti zuwa N2,400 a kasuwa.
Masu zafi
Samu kari