Latest
Gwamnan jihar Ribas, Similanayu Fubara da tsohon gwamnan da ya gaba, Nyesom Wike, ministan Abuja sun haɗu sun gaisa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Kotun ɗaukara ƙara ta zartar da hukunci kan soke takarar ɗan takarar gwamnan APC na jihar Bayelsa. Kotun ta warware hukuncin soke takarar Timipre Sylva.
Gwamnatin jihar Rivers ta musanta rahotannin cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya kori shugaban ma'aikatansa da bayar da umarnin korar shugabannin kananan hukumomi.
Wasu 'yan bindiga sun yi ajalin wani mai sarautar gargajiya tare da sace matarsa da dansa da kuma wasu mutane takwas a kauyukan da ke makwabtaka da su.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya umarci tantance karin mutane 147 don yi mu su auren gata a jihar kamar yadda aka yi a baya na aurar da mutum 1,800.
An gano rikicin siyasar jihar Ribas yana da nasaba da matakin da Gwamna Siminalayi Fubara ya dauka na farfado da manufar Rotimi Amarchi, wannan ya fusata Wike.
Wata matar aure ta haifi tagwaye kasa da awanni 24 bayan mijinta ya mutu. Bidiyon matar da yaran nata ya tsuma zukatan mutane da dama a soshiyal midiya.
Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar kamo daliban firamare 2 da suka cinna wa makarantarsu wuta a jihar Ogun, rundunar ta ce ta fara bincike kan wannan danyen aiki.
Kotun daukaka kara reshen Abuja ta tabbatar da Natasha Akpoti-Uduagan a matsayin sahihiyar yar takarar da ta lashe zaben sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya.
Masu zafi
Samu kari