Latest
Rundunar 'yan sanda ta kama dan takarar gwamna a jam'iyyar NNPP a 2023, Wilfred Bonse kan zargin damfarar wani kamfani naira miliyan 607 a Kuros Riba.
Jam'iyyar NNPP mai kayan alatu ta yi zargin cewa wasu da ake ea laƙabi da yan bindigan da ba a sani ba suna barazanar kai hari babban sakateriyar jam'iyyar ta ƙasa.
Fasto David Ayuba Azzaman ya bayyana cewa an nuna masa cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu akwai wanda ke juya akalarta a cikin wani wahayi da ya samu.
Gwamna Babajide Sanwo Olu ya ware Naira miliyan 70 domin buga hotunan Tinubu a Legas, ana ta kukan babu kudi, amma da alama har yanzu ba a rage sharholiya ba.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa shi kan masarautun gargajiya sun fi masa ko wane bangare a Najeriya inda ya bayyana muhimmancinsu ga kawo hadin kai.
Tsohon ministan sufuri a Najeriya, Rotimi Amechi ya bayyana cewa ya tafka kuskure yayin da ya tura sunan Wike mukamin Minista a lokacin mulkinsa a jihar Ribas.
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi alkawarin saka wadanda su ka lashe gasar musabaka cikin jerin malamai ma su fadakarwa a aikin hajjin shekarar 2024.
Gwamnatin jihar jihar Osun ta haramta kaciyar mata a fadin jihar baki daya yayin da ta bayyana illolinta ga 'ya'ya mata inda ta gargadi jama'a kan wannar al'ada.
Dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi ya shiga sahun yan siyasa wajen taya Atiku Abubakar murna yayin da ya cika shekaru 77 a duniya. Ya kira shi da babban yayansa.
Masu zafi
Samu kari