Latest
Dakarun sojoji sun cafke wani fitaccen malamin addinin Musulunci mai suna Sheikh Muhammad Alkandawi da matarsa a Dei-Dei da ke birnin Abuja a ranar Talata.
Wasu matasa a yankin masarautar Okuku a jihar Kuros Riba sun nuna damuwa da halin sarkin yankinsu saboda ya ƙi ya shawo kan rikicin ƙabilancin da ke faruwa.
Gwamnan Ribas Siminalayi Fubara ya bayyana yadda ya yi fama da tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nweson Wike cikin shekara. Ya ce Wike ya bar masa bashi.
Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak ya yi magana kan cewa a yau ba sai mutum ya mallaki digiri zai yi nasara ba. Mutane na mayar masa da martani daga fadin duniya.
Wani binciken gaskiya da aka gudanar ya fayyace gaskiya kan ikirarin da wani shafin yanar gizo ya yi cewa Tinubu zai ba da tallafin N250,000 ga 'yan Najeriya.
Shugaban TUC na kasa, Festus Osifo ya ce ƴan kwadago za su iya saukowa ƙasa daga bukatarsu ta biyan N494,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.
Majalisar wakilan tarayya ƙarƙashin jagorancin Tajudeen Abbas ta lashi takobin gudanar da bincike kan yadda CBN ke korar ma'aikata barkatai da sunan gyara.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da sace ɗalibai mata biyu na jami'ar tarayya JOSTUM a Makurdi, babban birnin jihar Benue ranar Asabar da ta wuce da dare.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Abdulsalam Aminu Gwarzo ya kai ziyara wurin Sarki Muhammadu Sanusi II a fadarsa duk da umarnin Babbar Kotun Tarayya.
Masu zafi
Samu kari