Latest
Kotu ta sallami shugaban Miyetti Allah Kautal Kore Bello Bodejo daga tuhumar da ake masa na ta’addanci wanda ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya shigar.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda majalisar jamhuriya ta uku ta masa sharar fage wajen samun nasara a babban zaben shugaban kasa a shekarar 2023.
Kimar kuɗin Najeriya ta dawo yayin da Dalar Amurka ta sake yo ƙasa a kasuwar hada-hadar kuɗi ta bayan fage, haka abun yake a kasuwar da gwamnati ke kula da ita.
A yau Laraba 29 ga watan Mayu, Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da aka kirkira ta sauya taken Najeriya zuwa "Nigeria We Hail Thee".
'Yan ta'addan kugiyar ta'addanci ta ISWAP sun kai farmaki kan wasu masunta a jihar Borno. Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka mutum 15 a yayin harin.
Kwamitin dake tattaunawa kan mafi karancin albashi har sai baba ta gani ba tare da bayyana dalilin hakan ba. Kungiyar kwadago dai ta ki amincewa da tayin gwamnati.
Ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta roki kungiyoyin NLC da TUC kan suyi hakuri su karbi N60,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.
Shugaban kungiyar lauyoyi ya kasa (NBA) Yakubu Maikyau, OON, SAN ya bayyana yadda ake ta sabata juya ta da hukuncin kotu kan dambarwar masarautar.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a jihohin Borno da Katsina a Arewacin Najeriya.
Masu zafi
Samu kari