Latest
A wannan labarin, za ku ji wani matukin baburin adaidata sahu, Bashir Muhammad ya samu kyaututtuka bayan ya mayar da kayan da aka manta a baburinsa.
APC ta ce tana shirye kan zaben kananan hukumomi da za a yi a Kano a ranar 24 ga Oktoba. APC ta bukaci hukumar zabe ta Kano ta mata adalci yayin zaben.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya nemi yafiyar tsohon gwamna, Rashidi Ladoja kan wasu abubuwa da suka faru a baya inda ya ce ba shi da wata matsala da shi.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Akwa Ibom ta fara yajin aiki a fadin jihar. NLC ta fara yajin ne sakamakon tashin gwauron zabin da farashin fetur ya yi.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce za a yi shirin Arewa TECHfest a dukkan jihohin Arewa. ya ce za a farfado da fasahar zamani a Arewa. za a yi shirin a Katsina.
Rahotannin da muke samu sun nuna cewa Allah ya yiwa mahaifiyar tsohon shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa rasuwa a jihar Sakkwato ranar Laraba da daddare.
A wannan rahoton, hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce a shirye ta ke wajen fuskantar tsohon gwamnan Kogi, Bello Yahaya a kotu.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce dole sai yan Najeriya sun gyara halinsu kafin kawo karshen magudin zabe a Najeriya, ya ce na'urar zabe ta yi kadan.
Ana hasashen jam'iyyar APC za ta taka rawar gani a zabukan jihohin Ondo da Anambra da Osun da Ekiti da za a gudanar kafin babban zaben 2027 mai zuwa.
Masu zafi
Samu kari