Rundunar Sojin Isra'ila na Shirin Rugujewa ana Yakin Iran, an Gargadi Netanyahu

Rundunar Sojin Isra'ila na Shirin Rugujewa ana Yakin Iran, an Gargadi Netanyahu

  • Sojojin Isra'ila sun fara fitowa suna fadawa kansu gaskiya yayin da yakin da suke da kasar Iran ke cigaba ba tare da zuwa karshe ba
  • Babban hafsan sojin Isra’ila, Eyal Zamir ya yi gargadi da cewa rundunar sojojin kasar za ta iya rugujewa saboda wata matsala da ya hango
  • Wasu tsofaffin shugabannin kasar sun bukaci a fara daukar kowa ya shiga aikin soja domin kaucewa barazanar da ta tunkaro su a halin yanzu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Irsa'ila - Babban hafsan sojin Isra’ila, Eyal Zamir, ya yi gargadin cewa rundunar sojin ƙasar na iya fuskantar rugujewa idan gwamnati ba ta magance matsalar ƙarancin ma’aikata da ke ƙaruwa ba.

Rahotanni sun nuna cewa Eyal Zamir ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 25 ga Maris, 2026 yayin da suke cigaba da gwabza yaki da kasar Iran.

Kara karanta wannan

Yan Isra'ila sun fara gajiya da halin Netanyahu, sun soke shi kan yaki da Iran

Sojojin Irsa'ila suna tattaunawa
Eyal Zamir da wasu sojojin kasar Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Barazana a rundunar sojin Isra'ila

Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa kasar Isra'ila ta sanar da matsalar karancin sojoji kamar yadda hafsun sojan kasar ya fada a wani taro.

Yayin wani taron majalisar tsaro a ranar Laraba, Zamir ya ce:

“Ina da korafi kafin rundunar sojin Isra’ila ta rushe da kanta,”

Majiyoyin soji sun bayyana damuwa sosai kan ƙarancin ma’aikatan, musamman a yayin yaƙin da ake ciki yanzu, suna cewa ko a lokacin zaman lafiya ma ana bukatar ƙarin sojoji a wurare da dama kamar Gaza, Lebanon, Syria da sauransu.

Times of Israel ta wallafa cewa jami’ai sun yi gargadin cewa idan ba a samu karin sojoji ba, za a samu babban gibi a ayyukan tsaro a wurare daban-daban a fadin Isra'ila.

Me ke girgiza rundunar Isra'ila?

An danganta wannan matsala da rashin dokar da za ta faɗaɗa tilasta shiga aikin soja ga al’ummar haredi (wasu mabiya addinin Yahudanci masu tsattauran ra'ayi).

Kara karanta wannan

Amurka ta kira ruwa: Dakarun Iran na musamman sun shirya aikin bazata

An ce an dakatar da wani kudirin doka da aka gabatar domin ƙara yawan shigar haredi cikin soja na ɗan lokaci bisa umarnin Benjamin Netanyahu domin tabbatar da haɗin kai yayin yaƙi da Iran.

Benjamin Netanyahu a wajen taro
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin da 'yan adawa suka yi

‘Yan adawa sun soki gwamnati sosai bayan kalaman Zamir, suna gargadin cewa hakan na iya haifar da barazana ga tsaron ƙasa.

Mambobin jam’iyyar Yesh Atid sun bayyana dakatar da ƙoƙarin tilasta shiga soja a matsayin “barazana ga tsaro”, suna cewa:

“Ba za a iya ci gaba da watsi da wannan batu ba.”

Jagoran ‘yan adawa, Yair Lapid, ya ce:

“A gaba, gwamnati ba za ta iya cewa ba ta sani ba idan bala'i ya taso.”

Shugaban jam’iyyar Yisrael Beytenu, Avigdor Liberman, ya bukaci a tilasta wa kowa shiga aikin soja, yayin da tsohon Firaminista Naftali Bennett ya ce:

“Me kuke jira haka?”

An harbi jirgin Isra'ila a Lebanon

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa ta kai farmaki kan dakarun Isra'ila da suke cikin wani jirgin yaki a Lebanon.

Hakan na zuwa ne yayin da kungiyar ta nuna goyon baya ga Iran a yakin da Isra'ila ta hada kai da Amurka ta kaddamar a kan Tehran.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton Firaministan Isra'ila bai fito ya yi magana kan hakikanin abin da ya faru da jirgin ba ko halin da sojojin suka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng