Jarumar Fim Halima Ta Fito Tana Rusa Kuka, ba Ta da Lafiya kuma Ta Talaunce
- Jarumar Nollywood Halima Abubakar ta bayyana cewa tana fama da ciwon kwakwalwa tare da fuskantar matsanancin rashin matsuguni
- Ta ce ta kashe dukiyar da ta tara wajen yi wa mahaifiyarta tiyata da ta lakume Naira miliyan 9, lamarin da ya kara tsananta mata rayuwa
- Halima ta yi kira ga fitattun ’yan Najeriya da suka hada da Seyi Tinubu da al’umma baki daya da su taimaka mata da kudin jinya da matsuguni
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jarumar fina-finan Nollywood, Halima Abubakar, ta sake bayyana halin da take ciki na matsanancin rayuwa, inda ta ce tana fama da ciwon kwakwalwa tare da rashin matsuguni bayan an kore ta daga gidan haya.
Halima ta bayyana hakan ne yayin wani shirin kai-tsaye da ta yi, inda ta nuna damuwa da kunci, tana mai cewa halin da take ciki ya kai matakin neman taimakon jama’a saboda tsananin bukata.

Source: Twitter
TVC ta rahoto ta ce matsalolin sun taru ne bayan ta kashe duk kudin da take da su wajen jinyar mahaifiyarta, wanda hakan ya bar ta ba tare da isasshen abin dogaro ba a lokacin da ita ma take bukatar kulawar lafiya.
Jaruma Halima Abubakar ba ta da lafiya
Halima Abubakar ta bayyana cewa likitoci sun gano tana dauke da ciwon kwakwalwa, kuma tun daga lokacin take fama da jinya mai tsanani da kuma shan magunguna tsawon shekara guda.
The Cable ta rahoto ta ce duk da taimakon da aka taba tara mata domin jinyarta, ba ta samu damar amfani da kudin wajen biyan kudin hayar gidanta ba.
Jarumar ta ce wannan lamari ya bar ta ba tare da matsuguni ba, inda ta kwashe kayanta gaba daya ba tare da sanin inda za ta dosa ba, tana mai cewa halin ya jefa ta cikin damuwa da karayar zuciya.
Halima ta nemi agajin Seyi Tinubu
Cikin kuka, Halima ta ambaci sunayen wasu fitattun ’yan Najeriya, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, VeryDarkMan, da kuma Seyi Tinubu, tana rokon su da su taimaka mata.
Ta ce ta yi kokarin tuntubar wasu shahararrun mutane a masana’antar fim amma ba ta samu amsa ba, lamarin da ya kara jefa ta cikin fargaba da jin an yi watsi da ita.

Source: Instagram
Halima ta bayyana cewa ta taba janye kudin da aka tanadar mata domin tiyata ne don ta biya kudin haya, amma hakan ma bai yi nasara ba, wanda ya sa take neman taimako daga ’yan Najeriya baki daya.
Jarumar ta ce tana bukatar akalla Naira miliyan 25 domin gudanar da tiyata, cire sassan jiki da suka samu matsala, da kuma samun matsuguni da abinci.
Jarumar fim na bukatar mijin aure
A wani labarin, mun kawo muku cewa jarumar fim kuma mawakiya, Tamar Braxton ta nuna cewa lokaci ya yi da ya kamata ta yi aure.
Tamar ta bkoka da cewa ta kai shekara 48 ba tare da samun mijin da ya dace da ita ba, amma duk da haka kofar ta a bude take.
A hirar da aka yi da ita, jarumar ta kara da cewa ta san tana da hali na gari kuma ita mace ce wacce ba za a yi nadamar zama da ita ba.
Asali: Legit.ng

