Bayan Yiwa Shugaba Maduro Daukar Amarya, Amurka za ta Kwashe Man Fetur a Venezuela
- Shugaban kasar Amurka Trump ya jaddada aniyarsa ta tura kamfanonin Amurka domin kwashe man kasar Venezuela
- Amurka ta yiwa shugaba Maduro daukar amarya a kasarsa bayan zarginsa da manyan laifukan ta’addanci a kasar tasa
- Rahoto ya yi tsokaci kan yadda Amurka ta kakabawa kasar Venezuela takunkumi mai karfi kan albarkatun man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a ranar Asabar ya ce zai ba kamfanonin man fetur na Amurka damar shiga Venezuela domin hako dimbin man da kasar ke da shi.
Wannan na zuwa ne bayan wani samame da sojojin Amurka suka kai kasar tare da kama shugaban kasar, Nicolas Maduro, kamar yadda Trump ya nuna a shafukansa na sada zumunta.
Sojojin Amurka sun kai jerin hare-haren sama a birnin Caracas, babban birnin Venezuela, da sassafe ranar Asabar.

Source: Getty Images
Yadda aka kama shugaba Maduro a kasarsa
An kama Maduro tare da matarsa, sannan aka kaisu birnin New York na Amurka, inda ake tuhumarsu da laifukan safarar miyagun kwayoyi da makamai.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Kotu ta maye gurbin Shugaban Venezuela bayan Amurka ta kama shi
A cewar Trump:
“Za mu shigar da manyan kamfanonin man fetur na Amurka, mafi girma a ko’ina cikin duniya, su zuba biliyoyin daloli, su gyara abubuwan more rayuwa da suka lalace sosai, musamman na man fetur, sannan su fara samar wa kasar kudaden shiga.”
Trump ya kuma jaddada cewa “haramcin shigo da duk wani man fetur daga Venezuela na nan daram.”
Takunkumin da Amurka ta kakabawa Venezuela
Amurka ta kakaba takunkumin tattalin arziki kan Venezuela tun shekarar 2017, sannan daga bisani ta kara da takunkumin man fetur bayan shekaru biyu.
A cewar Kungiyar Kasashen da ke Fitar da Man Fetur (OPEC), Venezuela na samar da akalla ganga miliyan daya na man fetur a kullum, inda mafi yawansa ake sayar da shi a kasuwar bayan fage da rangwame mai yawa.
Trump ya yi ikirarin cewa Caracas na amfani da kudaden man fetur wajen daukar nauyin “ta’addancin miyagun kwayoyi, safarar mutane, kisan kai da garkuwa da mutane.”
Matakan Trump kan kasashen duniya kan Venezuela
A farkon wa’adinsa na biyu a shekarar 2025, Trump ya soke lasisin da ke bai wa kamfanonin mai da iskar gas na kasashen waje damar aiki a Venezuela duk da takunkumin da aka kakaba, inda kamfanin Chevron na Amurka kadai ya samu rangwame.
Chevron na gudanar da ayyuka a filayen mai guda hudu a Venezuela tare da hadin gwiwar kamfanin gwamnati PDVSA da rassansa.
Haka kuma, Washington ta kakaba cikakken katanga kan tankokin mai da aka sanya wa takunkumi da ke shiga ko fita daga Venezuela.
Matakin man kasar Venezuela
A cewar Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (IEA) a shekarar 2023, kasar Venezuela na dauke da kusan 17% na ajiyar man fetur na duniya, sai dai ba ta cikin manyan kasashen da ke samar da mai saboda shekaru na tabarbarewar shugabanci da cin hanci da rashawa.
Man kasar Venezuela ba shi da inganci sosai, kuma yawanci ana sarrafa shi ne zuwa dizal ko wasu kayayyakin da ake samu daga mai kamar kwalta, maimakon fetur.
Amurka na da matatun mai a yankin Tekun Mexico da aka kera musamman domin sarrafa irin wannan mai.
Stephen Schork, wani manazarci a kamfanin ba da shawara na Schork Group, a wata hira da ya yi da AFP a watan da ya gabata, ya bayyana cewa dalilan siyasa ne suka fi rinjaye a lamarin. Inda ya kuma ce:
“Amurka na tafiya lafiya lau ba tare da man fetur na Venezuela ba.”
Asali: Legit.ng

