Fitaccen Jarumin kuma Furodusa a Kannywood ya Kwanta Dama
- Bayan kwanaki da rasuwar fitaccen jarumin barkwancin da aka fi sani da Kamal aboki, Ubangiji ya amsa rayuwan wani fitaccen jarumi kuma furodusa a masana'antar Kannywood
- Marigayin, Abdulwahab Awarwasa, ya kwanta dama ne bayan daukar tsawon lokaci yana jinya a garin Kano daga bisani wani uban gidansa ya dauke shi zuwa Jos
- Mamacin da ya rasu a garin Jos ya bar mata da 'ya'ya uku, kuma an yi jana'izar gawarsa a garin Kano, wanda rasuwar tasa ta kada zukatan jaruman Kannywood da dama
Kano - Da yammacin Litinin, 23 ga watan Janairun 2023, Allah ya amshi rayuwar wani tauraro kuma furodusa a masana'antar Kannywood, Abdulwahab Awarwasa.
Mamacin ya kwanta dama a garin Jos ne bayan fama doguwar jinya.
Abdulwahab Awarwasa dai dan asalin anguwar Fagge ne cikin birnin jihar Kano, wanda aka dade ana damawa da shi a harkar fim inda yake fitowa a matsayin dan sara suka kuma Ali Nuhu ne uban gidansa.
Yanzu-Yanzu: Wajibi Ne A Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Da Wata 6: Majalisar Dattawa Tayi Ittifaki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jarumin ya dauki tsawon lokaci yana shirya fina-finai Matsayin Awarwasa a masana'antar shirya fina-finai har ta kai ga zama furodusa.
Wata majiya mafi kusa da shi ta shaida wa mujallar Fim yadda ya dauki tsawon lokaci yana jinya a Kano, daga bisani wani uban gidansa ya dauke shi zuwa Jos don nema masa lafiya, wanda a nan ne sa'insa ya cika.
Marigayin ya rasu ya bar matar aure daya da 'ya'ya uku. An yi jana'izar gawarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a garin Kano.
Mutuwar tasa ta girgiza zukatan 'yan Kannywood, nda jarumai irin su Ali Nuhu, Maryam Booth, Umar M. Sharif, Aisha Humaira suka yi wallafa game da rasuwarsa.
Fatanmu shi ne, Ubangiji ya jikansa ya kuma gafarta masa kurakurensa yasa jinyar da yayi ta zame masa kaffara.
Abale zai angwance
A wani labari na daban, fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood, Daddy Hikima wanda ake kira da Abale ya shirya shiga daga ciki.
Jarumai masu tarin yawa sun sanar da daurin aurensan ta hanyar wallafa katin auren.
Za a daura ne a Na'ibawa a Masallacin Juma'a na Uhud a ranar 27 ga watan Janairun 2023.
Asali: Legit.ng