Kannywood: Jaruma Hadiza Gabon ta musanta zargin ta yi wa masoyinta alƙawarin aure
- Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta gurfana a gaban Kotun Shari'ar Musulunci da ke Magajin Gari a Kaduna kan tuhumar da ake mata
- Jarumar ta faɗa wa Kotu cewa ba ta san mutumin ba, wanda ya kai ta ƙara bisa zargin ta masa alƙawarin aure bayan ya kashe mata kudi
- Gabon ta musanta tuhumar inda ta ce bata taba haɗuwa da shi ba kuma babu wata alaƙar soyayya a tsakanin su
Kaduna - Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta musanta sanin ma'aikacin nan ɗan shekara 48, Bala Musa, wanda ya yi ikirarin ta masa alƙawarin aure.
Daily Trust ta rahoto cewa mutumin ya bayyana cewa ba ya shayin tura mata kuɗi duk lokacin da ta nema kuma ta yi alƙwarin zasu yi aure bayan kashe mata N396,000.
Jarumar wacce ta bayyana a gaban Kotun Shari'ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari Kaduna ranar Talata, ta faɗa wa Kotun cewa ba ta san mutumin da ake magana a kan shi ba.
Da take jawabi ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, a harabar Kotun, Gabon ta musanta tuhumar da ake mata baki ɗaya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lauyan ya ce:
"Bayan ta saurari zargin da ake mata, jarumar ta yi nata jawabin wanda a cewarta, ba ta taɓa haɗuwa da shi ba, bama ta san abun da ya faru ba. Ya haɗu da ita a Facebook amma bamu san komai ba."
"Saboda haka ba mu san abin da yake ikirari ba, be dame mu ba, mun kuma saurare shi, yanzu mun bar kotu ta yanke hukunci."
Mutumin ya faɗa wa Kotu yadda suka haɗu da Gabon
Aikin Allah: Bidiyon yadda wani mutumi ya shiga ya tuƙa Tankar Fetur mai ci da wuta don ya ceci mutane
A ɗaya bangaren, lauyan wanda ya shigar da ƙara, Barista N. Murtala, ya ce wanda yake karewa ya haɗu da Gabon a Facebook, daga nan suka zama abokai.
Ya ƙara da cewa ta yi alƙawarin zata aure shi shiyasa yafara kashe mata kuɗi ba tare da jin komai ba.
"A facebook suka haɗu, daga nan suka zama abokai kuma buduwar ta yi alƙawarin zata aure shi, shi kuma ya fara kashe mata kuɗi, amma mun faɗa wa Kotu zamu gabatar da shaidu kan haka."
Wane mataki Kotu ta ɗauka?
Daga nan, Alƙalin Kotun Mai Shari'a Malam Rilwanu Kyaudai, ya ɗage zaman zuwa ranar 28 ga watan Yuni, 2022.
Ya kuma bai wa Jaruma Hadiza Gabo beli bisa sharaɗin zata gabatar da masu tsaya mata kuma mazauna cikin jahar Kaduna.
A wani labarin kuma Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023
Wasu daga cikin Jaruman Kannywood da tauraruwarsu ke haskawa sun bayyana tsayawa takarar siyasa a zaɓen 2023.
Mun tattaro muku waɗan nan jaruman da suka nuna sha'awar ba da gudummuwarsu a ɓangaren shugabancin al'umma a Najeriya.
Asali: Legit.ng