Rahama Sadau ta sadaukar da dukkan kudin da fim dinta na Nadiya zai kawo ga gidauniyar mabukata
- Jaruma Rahama Sadau ta sadaukar da dukkan cinikin da za ta yi a fim din ta mai suna Nadeeya ga gidauniyar tallafawa mabukata
- A hirar da aka yi da jarumar, ta sanar da cewa cinikin fim din kai tsaye za ta mika shi domin tallafawa masu karamin karfi a gidauniyarta ta Ray of Hope
- Ba wannan ne karo na farko da jarumar ta fara taimako, ko a lokacin annobar korona an gan ta da Fati Washa suna rabawa jama'a kayan abinci don rage radadi
Rahama Sadau, ta sadaukar da dukkan cinikin fim din ta na Nadeeya ga gidauniyar taimakawa mabukata da gajiyayyu.
Labarin da Legit.ng ta tattaro daga shafin Labaran Kannywood a Twitter shi ne: A wata tattaunawa ta kai tsaye da gidan talabijin da rediyo na Liberty ya yi da jaruma Rahama Sadau, ta sanar da cewa duk cinikin da ta yi a fim din ta da ake haskawa a sinima yanzu haka ta sadaukar da shi ga gidauniyarta ta tallafawa mabukata mai suna Ray of Hope.
Mahaifiyata da mijina sun yi shekaru 15 suna lalata: Mata ta fashe da kuka yayin bada labari a bidiyo
Wannan gidauniya mai suna Ray of Hope ta Rahama Sadau, ta kan taimakawa mabukata lokaci zuwa lokaci musamman a lokacin tsananin bukata wanda a baya mun taba ganin jarumar ta fito tare da kawar ta Fati Washa suna raba kayan abinci ga talakawa a lokacin annobar korona da sauran lokuta mabanbanta.
Shafin Labaran Kannywood a Twitter sun wallafa wani bangare na hirar inda Rahaman ke bayanin irin ayyukan da gidauniyar ta ke yi gami da rubuta:
"A tattaunawar da ake yi yanzu kai tsaye da jaruma Rahama Sadau a LibertyTVNews, ta sanar da cewa ta sadaukar da duk cinikin da fim din ta na Nadeeya yayi ga gidauniyar ta ta tallafawa marasa karfi Ray Of Hope.
"Wannan muhimmin abu ne da ya cancanci jinjina."
Ga bidiyon tattaunawar:
Shafin gidauniyar ta Ray of Hope sun wallafa inda suke wa Rahama Sadau godiya kan wannan abun alkhairi da ta yi inda suka yi alkawarin yin abun da ya dace da duk abin da aka samu.
Bidiyon katafaren Masallacin da Jaruma Hadiza Gabon ta gina saboda Allah
A wani labari na daban, a daren ranar Asabar ne wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram mai suna Kabir Idris Kura ya wallafa bidiyon wani masallaci da aka fara gininsa tun daga tushe har aka kammala shi.
Bawan Allan ya wallafa, "Alhamdulillah, wannan ne masallacin da jaruma Hadiza Gabon ta ginawa bayin Allah domin yin sallah fisabilillah.
"Ginin ya kammala kuma muna mata addu'ar Allah ta'ala yasa mata a mizaninta, ya kuma saka mata da alkhairi, ya ji kan mahaifinta Malam Aliyu Diya."
Asali: Legit.ng