Mutane na son ganin ƙarshen mu da taurin bashi, Jarumar Kannywood ta koka

Mutane na son ganin ƙarshen mu da taurin bashi, Jarumar Kannywood ta koka

  • Jarumar Kannywood, Sadiya Kabala, ta koka kan yadda mutane ke da taurin bashi idan ka amince ka ba su kayan ka
  • Jarumar tace da kasuwanci ne suke samu suna tsira da mutuncin su, musamman idan suka daina harkar shirin fim
  • Ta bayyana cewa rashin kama sana'a ke sa matan Kannywood shiga halin ƙaƙanikayi a baya, idan ta Allah tasa sun fito gidan aure

Mafi yawan jarumai mata a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, na shiga harkokin kasuwanci lokacin da zaren su ke ja a harkar fim da bayan sun ja baya.

Jaruma Sadiya Kabala, ta shaida wa BBC Hausa a wata hira cewa, jarumai mata na rungumar sana'a ne domin tsira da mutuncin su ko da bayan sun bar harkan fim.

Jaruma Sadiya na ɗaya daga cikin jarumai mata a Kannywood da suka fice daga harkar fim, kuma suka koma kasuwanci.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

Jaruma Sadiya Kabala
Mutane na son ganin ƙarshen mu da taurin bashi, Jarumar Kannywood ta koka Hoto: @Real_sadiya_kbl
Asali: Instagram

A cewar Sadiya Kabala, a can baya Jarumai mata a Kannywood na shan baƙar wahala idan suka bar masana'antar, sabida basu tunanin yin wata sana'a bayan shirin fim yayin da tauraruwar su ke haskawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sadiya tace:

"Idan ka yi la'akari da jarumai mata a can baya, fim din kawai suka sa a gaba. Shiyasa sai kaga idan sun yi aure, ta Allah takasance sua fito, sai kaga sun dawo basu da abun yi."

Wane kalubale kuke fama da shi a kasuwancin ku?

Sai dai Sadiya ta bayyana cewa babban kalubalen da suke fuskanta a harkar kasuwancin su shi ne kwastomomi masu ɗaukar bashi.

A cewarta mutanen yanzu ba su da tausayi, kana sana'arka, wanda ya kamata ya taimake ka amma shi ne zai kokarin ganin bayan ka.

"Mutum zai zo da kamalan shi da komai, kuma yafi karfin abu, ga shi kin sanshi yana da kima, ya karbi kayan da muke siyarwa yace zai bada kudin."

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

"Daga baya ki gama kiran mutum, wani ma ko magana mai daɗi ba zai maka ba. Gaskiya ba karamar illa masu taurin bashi ke mana ba."

A wani labarin na daban kuma Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

A wannan makon an samu wasu muhimman abubuwa guda 5 masu muhimmanci da suka faru a Kannywood.

Daga cininsu shine batun raɗin sunan jaririyar da aka haifa wa Adam Zamgo, da kuma abinda ya shafi Rahama Sadau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: