Babbar Magana: Iran Ta Yi Barazana kan Sabon Matakin da Amurka Ta Dauka
- Amurka ta dauki matakin hana zirga-zirga a tashoshin jiragen ruwan Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Rundunar sojojin Amurka ta ce za ta dauki matakin rufe tashoshin jiragen ruwan ne daga ranar Litinin, 13 ga watan 2026
- Sai dai, rundunar sojojin Iran ta fito ta bayyana abin da zai faru muddin Amurka ta kulle tashoshin jiragen ruwan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar sojin ƙasar Iran ta yi martani kan matakin Amurka na killace tashoshin jiragen ruwanta.
Rundunar sojojin ta bayyana cewa duk wani yunƙuri na killace zirga-zirgar jiragen ruwa da Amurka ta sanar a fadin duniya ya saɓa wa doka kuma tamkar fashi da makami ne.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton gargadi da rundunar ta yi a ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026.
Iran ta yi gargaɗin cewa babu wata tashar jiragen ruwa a yankin Tekun Gulf da za ta kasance cikin aminci muddin aka yi barazana ga nata tashoshin.
Amurka ta killace tashoshin jiragen Iran
Rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa za ta fara killace dukkan tashoshin jiragen ruwan Iran ne a yau Litinin da misalin ƙarfe 14:00 GMT (ƙarfe 3:00 na rana a agogon Najeriya), bayan da tattaunawar da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu a Pakistan ta ruguje.
Shugaba Donald Trump shi ma ya sanar a shafukansa na sada zumunta cewa Amurka za ta rufe mashigar Hormuz, wadda yake buƙatar Iran ta buɗe ta gaba ɗaya.
Me sojojin Iran suka ce?
Tashar Press tv ta ce wata sanarwa da sojojin Iran suka fitar a yau Litinin ta ce:
"Idan har aka yi barazana ga tsaron tashoshin jiragen ruwan Iran da ke cikin ruwan Tekun Fasha da Tekun Arabian Sea, babu wata tashar jiragen ruwa a waɗannan yankuna da za ta kuɓuta."
Sanarwar, wadda hedikwatar tsaron Iran ta Khatam al-Anbiya ta fitar kuma aka karanta a gidan talabijin na ƙasar, ta ƙara da cewa:
“Takunkumin da Amurka mai aikata laifuffuka ta sanya wa zirga-zirgar jiragen ruwa a ruwan duniya ya saɓa wa doka, kuma misali ne na aikin fashi da makami.”
An kasa cimma yarjejeniyar sulhu
Rashin nasarar tattaunawar da aka yi a ƙarshen mako ya ruguza fatan samun yarjejeniyar dindindin ta kawo ƙarshen yaƙin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da jefa tattalin arziƙin duniya cikin tangal-tangal tun lokacin da aka fara shi a ƙarshen watan Fabrairu.
Duk da waɗannan barazana, yarjejeniyar tsagaita wutar da aka ƙulla tsakanin Amurka, Isra'ila, da Iran a makon jiya har yanzu tana aiki, kuma babu wata alama da ke nuna cewa za a koma fagen yaƙi nan take.

Source: Facebook
Zirga-zirga ta mashigar Hormuz, wadda take da muhimmanci sosai ga jigilar mai da iskar gas na duniya, ta fuskanci matsala tun farkon yaƙin, inda Iran ke barin wasu tsirarun jiragen ruwa na ƙasashe ƙawayenta kamar China kaɗai su wuce.
Wannan sabon mataki na Amurka na iya zama sanadiyar ƙaruwar farashin mai a duniya da kuma sake fuskantar barazanar barkewar yaƙi gaba ɗaya.
Birtaniya ta juyawa Amurka baya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta shiga cikin shirin Amurka na killace tashoshin jiragen ruwan Iran ta hanyar amfani da dakarun soji ba.
Starmer ya jaddada cewa ba za a yi amfani da jiragen yaƙi ko sojojin Birtaniya wajen toshe hanyoyin ruwan Iran ba.
Ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ganin an buɗe mashigar ruwa ta Hormuz baki ɗaya domin rage farashin makamashi cikin gaggawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


