Trump Ya ba Duniya Mamaki, Ya Fito Kamar Yesu Almasihu a Hoto

Trump Ya ba Duniya Mamaki, Ya Fito Kamar Yesu Almasihu a Hoto

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya dauki hankalin duniya da ya wallafa hoton kansa a irin wata shiga da ta yi kama da ta Yesu Almasihu
  • Hakan na zuwa ne sa'o'i bayan Trump ya caccaki Fafaroma Leo a wani dogon rubutu da ya yi yana cewa bai san harkokin kasa da kasa ba
  • Alakar Trump da Fafaroma ta fara tsami ne tun bayan caccakar da Leo ke yi wa Amurka kan kai farmaki Iran da wasu kasashen duniya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Donald Trump ya wallafa hoton AI da ke nuna shi a matsayin Yesu Almasihu bayan ya soki Fafaroma Leo, inda ya siffanta shi da mutum mai rauni.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun sabani tsakanin Donald Trumo da Fafaroma kan yake-yake da Amurka ke yi.

Kara karanta wannan

Trump ya yi wa Fafaroma Leo wankin babban bargo bayan masa nasiha kan Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump ya saka hoton da ke nuna shi tamkar Yesu Almasihu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton jaridar the Independent ya nuna cewa Donald Trump ya wallafa hoton ne jim kadan bayan ya fito karara ya caccaki Fafaroma Leo.

Trump ya saka hotonsa a matsayin Yesu

Shugaba Donald Trump ya wallafa hoton AI da aka nuna shi cikin tufafin da ke nuna alamar addinin Kirista, yana kewaye da haske.

A hoton, an hango Trump a gaban wani mutum a kwance yana nuna kamar yana warkar da wani da ba shi da lafiya kamar yadda Yesu ya ke yi.

A hoton, an ga Trump tare da wasu mutane da za a iya fassara su da mala’iku tare da sojoji a gefensu da tutar Amurka a bayan su.

Haka kuma jiragen yaki na shawagi a sama suna barin hayaki, yayin da ake ganin wuta, abin da ke nuna karfin soja da Trump ke alfahari da shi.

Donald Trump da Fafaroma Leo
Shugaba Donald Trump a hagu da Fafaroma Leo a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kuma hango wani mutum-mutumi da ke kara nuna alamar kasar Amurka a bayan Trump da mutanen da ke cikin hoton da aka wallafa.

Kara karanta wannan

Trump Ya Fadi abin da Zai Faru da China idan Ta Kuskura Ta Tura wa Iran Makamai

Asalin rikicin Trump da Fafaroma

Rahoton WIO News ya nuna cewa adawar Trump da Fafaroman ta samo asali ne daga kalaman da Leo ya yi kan yakin Iran da Amurka ta hada kai da Isra'ila ta kaddamar.

Tun bayan fara yakin, Fafaroma Leo ya kira yakin da rashin adalci tare da sukar barazanar Trump na lalata gaba dayan Iran a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.

Haka kuma ya soki manufofin gwamnatin Trump kan korar bakin haure da kuma hare-haren jami’an ICE, yana cewa yadda ake mu’amala da bakin haure ya saba mutuncin dan Adam.

Fafaroma ya kuma ki amincewa da gayyatar Trump na shiga abin da ya kira “Kwamitin Zaman Lafiya” na Gaza, sannan ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Amurka a watan Yuli 2026 domin bikin cika shekaru 250 na kasar.

Abokin Trump ya fadi zabe

A wani labarin, mun kawo muku cewa abokin Shugaba Donald Trump ya sha kaye a zaben Firaminista da aka yi a kasar Hungary.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Iran ba, Trump ya sake barazana kan kwace Greenland

Abokin Trump, Viktor Orban ya sha kaye ne duk da gagarumin alkawarin da Amurka ta yi wa Hungary idan aka sake zaben shi a bana.

'Yan Amurka da suka hada da manyan 'yan siyasa da 'yan kasuwa sun yi martani kan nasarar da aka samu a kan abokin Donald Trump.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng