An Barke da Murna bayan Kayar da Abokin Trump a Zaben Kasar Hungary
- Na hannun daman shugaba Donald Trump, Viktor Orban da ke rike da mukamin Firaminstan kasar Hungary ya sha mummunan kaye a zabe
- 'Yan jam'iyyar Democrat a kasar Amurka sun barke da murna, inda suka rikar fitar da sakonnin da za su iya fusata shugaba Donald Trump
- Baya ga 'yan siyasar kasar, 'yan Amurka da dama sun yi martani kan da faduwar abokin Trump a zabe, ciki har da mai kudin duniya, Elon Musk
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - ‘Yan jam’iyyar Democrat a Amurka sun yi murna bayan shan kayen Firaministan Hungary, Viktor Orban a ranar Lahadi,12 ga Afrilun 2026.
A gefe guda kuma, magoya bayan shugaba Donald Trump da ‘yan jam’iyyar Republican sun yi martani da ya nuna rashin jin dadin faduwarsa.

Kara karanta wannan
Halin da mazauna Iran ke ciki bayan sanar da tsagaita wuta tsakanin kasar da Amurka

Source: Getty Images
Kafar labarai ta Reuters ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da manyan mutane da 'yan siyasar Amurka suka fada bayan abokin Trump ya sha kaye.
Trump ya so Orban ya ci zabe
Trump ya mara wa Orban baya kafin zaben, har ma ya yi jawabi a wani gangamin yakin neman zabe a Hungary a makon da ya gabata.
Sai dai duk da haka Orban ya rasa mulki bayan shekaru 16, yayin da ‘yan Hungary suka kada kuri’u da yawa domin goyon bayan sabon Firaminista mai alaka da Tarayyar Turai, Peter Magyar.
An barke da murna a Amurka
Rahotanni sun nuna cewa 'yan majalisar dokoki daga manyan jam’iyyun Amurka biyu sun taya Magyar murna bisa nasarar da ya samu.
Wasu daga cikin ‘yan Democrat sun bayyana kayen Orban a matsayin alamar abin da zai iya faruwa a zaben Amurka na watan Nuwamban 2026.
“Ka kula, Donald Trump. Mutane ba su son masu son zama 'yan kama-karya,”
In ji shugaban ‘yan Democrat na majalisar dattawa, Chuck Schumer.
“Mai tsattsauran ra’ayi Viktor Orban ya sha kaye. Masu goyon bayan Trump da masu tsattsauran ra’ayin MAGA a majalisa su ne na gaba a watan Nuwamba,”
In ji shugaban ‘yan Democrat na majalisar wakilai Hakeem Jeffries.

Source: Getty Images
Trump ya yi gum kan zaben
Shi kansa Trump bai yi magana kan zaben Hungary a ranar Lahadi ba, duk da cewa ya yi tsokaci kan wasu batutuwa a shafukan sada zumunta da kuma hira da ‘yan jarida.
Sai dai wasu daga cikin abokansa masu goyon bayan Orban, irin su attajirin duniya, Elon Musk, sun nuna rashin jin dadinsu kan sakamakon.
“Kungiyar George Soros ta karbe Hungary,”
In ji Musk a shafinsa na X.
Alakar Trump da Orban
Wasu rahotanni sun nuna cewa Orban ne shugaba a kasashen Turai na farko da ya mara wa Donald Trump baya a zaben 2016.
A makon da ya gabata, Trump ya ce gwamnatinsa a shirye take ta yi amfani da dukkan karfin tattalin arzikin Amurka domin karfafa tattalin arzikin Hungary idan Orban ya yi nasara.
Trump ya caccaki Fafaroma Leo
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya caccaki Fafarom Leo a wani dogon rubutu da ya fitar.
Trump ya bayyana cewa Fafaroman ba shi da kwarewa a harkokin kasashen waje da yaki da ta'addanci, inda aya bukaci ya kame bakinsa.
Fafaroma ya sha sukar Trump kan yadda ya ke fitar da barazanar kai hare-hare Iran da kuma kai farmaki kasar Venezuela a farkon 2026.
Asali: Legit.ng

