Ba a Gama da Iran ba, Trump Ya Sake Barazana kan Yankin da zai Kwace a Duniya
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake barazana kwace tsibirin Greenland ke kasar Denmark bayan tsagaita wuta a yaki da aka yi da Iran
- Trump ya yi maganar ne jim kadan bayan tattaunawa da Shugaban NATO, Mark Rutte a fadar White House kan wasu muhimman abubuwa
- Kasashen da ke kungiyar NATO sun yi kokarin hana Donald Trump mallakar tsibirin Greenland a baya duk da ya nuna matukan son hakan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki kungiyar NATO tare da sabunta barazanar da ya taba yi kan Greenland bayan wata ganawa ta sirri da shugaban kungiyar, Mark Rutte.
Donald Trump ya tattauna da shugaban NATO yayin da kalamansa suka nuna yiwuwar ficewar Amurka daga muhimmin kawance na tsaron da suka kulla tsawon shekaru.

Kara karanta wannan
Faransa ta sako Netanyahu a gaba, ta kira Trump da Iran kan harin Isra'ila a Lebabon

Source: Getty Images
Legit Hausa ta tattaro bayanan da shugaba Donald Trump ya yi game da tsibirin Greenland ne a wani sako da Fadar White House ta wallafa a X.
Donald Trump ya yi barazana ga Greenland
Fushin Trump kan kasashen NATO saboda rashin shiga yakin Iran ya kara haifar da tsoron cewa zai iya janye Amurka daga wannan kawance na kusan shekaru 80.
Bayan ganawa da tawagar NATO, a cikin kalamansa na farko, ya sake nuna rashin jin dadinsa tare da barazana ga tsibirin Greenland
“NATO ba ta tsaya mana ba lokacin da muke bukatar su, kuma ba za su tsaya ba idan muka sake bukatar su,”
In ji shi.
“Ku tuna Greenland, wannan babban wuri mai dusar kankara da ba a kula da shi yadda ya kamata!!!”
Trump ya kara da wannan ba, ba tare da karin bayani ba.
Barazanar Trump kafin yakin Iran
Kafin Trump ya fara yakin Iran, barazanar da ya yi na kwace tsibirin Greenland daga hannun Denmark, duk da mamba ce a NATO, na daga cikin manyan batutuwan da suka tayar da kura a cikin kungiyar.

Kara karanta wannan
Tun ba a je ko'ina ba, Shugaba Trump ya canza tsarin tattaunawar Amurka da kasar Iran
Shugaban NATO kuma tsohon Firaministan Netherlands, Mark Rutte da ake kira “mai shawo kan Trump” saboda kwarewarsa wajen mu’amala da shugaban Amurka ya shiga fadar White House, inda aka gudanar da ganawa ta bayan fage.
“Ganawa ce mai cike gaskiya kuma tattaunawa abubuwa a bayyane,”
In ji Rutte kamar yadda the Hindu ta rahoto.
Lokacin da aka tambayi Mark Rutte ko Shugaba Donald Trump ya bayyana niyyarsa ta ficewa daga NATO, bai ba da amsa kai tsaye ba.

Source: Getty Images
Mai magana da yawun fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce yiwuwar ficewa daga NATO wani abu ne da shugaban ya taba tattauna shi da Rutte.
Amurka ta yi gargadi kan Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Amurka ta fitar da sabon rahoton tsaro game da halin da ake ciki a jihohin Najeriya.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bukaci ma'aikatan da ke aiki a ofishin jakadancinta da ke Abuja da su shirya tafiya gida tare da iyalansu.
Ta kuma lissafa jihohin Taraba, Yobe, Filato, Yobe, Bayelsa, sauransu kan cewa suna da hadarin da bai kamata 'yan Amurka su ziyarce su ba.
Asali: Legit.ng