An Saka Rana da Wajen da Iran za Ta Tattauna da Amurka bayan Tsayar da Yaki

An Saka Rana da Wajen da Iran za Ta Tattauna da Amurka bayan Tsayar da Yaki

  • Kasar Pakistan da ta shiga tsakani wajen dakatar da yakin Iran da Amurka/Isra'ila na mako biyu ta yi karin haske kan matakai na gaba da za a dauka
  • Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya sanar da rana da wajen da za a hadu da wakilan kasashen da suke yaki domin tattaunawa da juna
  • Shehbaz Sharif ya bayyana cewa dukkan bangarorin sun yi amfani da hikima, kuma yana fatan a samu matsaya mai kyau bayan sun hadu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Pakistan - Tsagaita wuta na mako biyu tsakanin Amurka da Iran ya dakatar da hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a kan Iran.

Yarjejeniyar da Pakistan ta shiga tsakani wajen samar da ita ta biyo bayan munanan hare-haren jiragen sama, makamai masu linzami da barazana da suka hada da hare-haren da ba a taba ganin irinsu ba a kasashen yankin Gulf.

Kara karanta wannan

Yakin Iran/Isra'ila: Yawan asarar da Amurka ta yi yayin yaki a Gabas ta Tsakiya

Mojtaba Khamenei da Donald Trump
Mojtaba Khamenei a dama da Donald Trump a gefen hagu. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Bayanin Firaministan kasar Pakistan

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya yabawa kasashen a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X yayin da yake sanar da tsagaita wutar.

“Bangarorin biyu sun nuna hikima da fahimta mai kyau, kuma sun ci gaba da tattaunawa domin bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali,”

Iran ta tabbatar da cewa za ta ba da damar sake bude mashigar Hormuz ga jiragen ruwa a cikin mako biyun, lamarin da ya rage tangardar da ta haddasa tashin farashin mai da iskar gas a duniya.

Sai dai duk da haka, tambayoyi da dama na nan, yayin da Washington da Tehran ke da sabanin ra’ayi sosai kan abin da ya kamata ya zama cikakkiyar yarjejeniya.

Rana da wajen tattaunawar Amurka da Iran

Ana sa ran fara tattaunawa a birnin Islamabad na Pakistan a ranar Juma’a, inda za a ga ko tsagaita wutar za ta iya zama yarjejeniya mai dorewa.

Kara karanta wannan

Halin da mazauna Iran ke ciki bayan sanar da tsagaita wuta tsakanin kasar da Amurka

Firaministan Pakistan ya ce:

“Ina gayyatar wakilansu zuwa Islamabad a ranar Juma’a, 10 ga Afrilu, 2026, domin ci gaba da tattaunawa don cimma yarjejeniya ta karshe da za ta warware dukkan sabani.”
“Muna fatan cewa tattaunawar Islamabad za ta yi nasara wajen samar da zaman lafiya mai dorewa, kuma muna fatan jin karin labarai masu dadi nan gaba kadan.”
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif
Shehbaz Sharif a wajen wani taro a Saudiyya a 2025. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayanin masani daga kasar Iran

Wani masani kan siyasar duniya, Trita Parsi, ya ce tattaunawar da ake shirin yi a Islamabad na iya fuskantar matsala, amma yanayin na iya sauyawa.

Al-Jazeera ta rahoto ya koka da wasu dabi'u na Shugaban Amurka:

“Gazawar Trump wajen amfani da karfi ta rage karfin barazanar sojan Amurka, tare da kawo sabon yanayi a diflomasiyyar Amurka da Iran.”

Isra'ila ta rusa sharadin sulhu

A wani labarin, kun ji cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan sulhun da aka yi tsakanin Amurka da Iran domin tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Shirin tsagaita wuta tsakanin Iran, Amurka ya kawo gagarumin sauyi a duniya

Duk da cewa ya amince da wasu sharudan, Netanyahu ya nuna cewa bai san da maganar dakatar da kai hare-hare zuwa kasar Lebanon ba.

Sai dai kasar Pakistan da ta shiga tsakani ta sanar da cewa tsayar da kai hare-hare Lebanon na cikin sharudan da Donald Trump ya amince da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng