Matsala Sabuwa: An Fara Maganar Tsige Trump a Amurka kan Yakin Iran
- Yayin da aka samu matsaya kan tsagaita wuta a yakin Iran da Amurka, wata 'yar majalisar kasar, Ilhan Omar ta fara maganar tsige Donald Trump
- Ta mika bukatar gaggawa ga Shugaban majalisar Amurka tana neman a dawo zama domin tattauna batun tsige shi a hukumance
- Hakan na zuwa ne bayan barazanar shafe Iran a doron kasa da Trump ya yi, wanda ya sha suka daga ƙasashen duniya da wasu shugabanni
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka - Alamu sun nuna cewa shugaban Amurka, Donald Trump zai fuskanci barazanar siyasa bayan yakin Iran da ya kaddamar a Gabas ta Tsakiya.
Duk da sanar da tsagaita wuta, wasu 'yan siyasar Amurka sun caccaki Trump kan barazanar shafe Iran a doron kasa da ya yi a ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026.

Source: Getty Images
Legit Hausa ta rahoto cewa 'yar majalisar Amurka, Ilhan Omar ta yi kira a tsige shugaba Donald Trump a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.
Maganar tsige Donald Trump a Amurka
‘Yar majalisar dokokin Amurka, Ilhan Omar, ta bayyana cewa akwai bukatar tsige shugaba Donald Trump daga shugabancin da ya ke yi a kasar.
Ta ce:
"Dole ne a tsige Donald Trump daga kan mulki saboda barazanar aikata laifuffukan yaki da kisan kare dangi."
A ranar Talata Trump ya bayyana cewa zai kai munanan hare-hare kasar Iran, musamman kan tashoshin lantarki da sauran abubuwan more rayuwa.
Trump ya yi barazanar kai harin da zai kawo karshen Iran a duniya, lamarin da ya jawo masa suka daga ƙasashe da shugabannin duniya, ciki har da 'yan Amurka.
Kira a fara zama a Majalisar Amurka
Rahotanni sun nuna cewa Ilhan Omar ta yi kira ga shugaban majalisar kasar da a dawo aiki domin fara tattauna batun tsige Donald Trump.
Ta ce:
"Shugaba Johnson, ya kamata a dawo zaman majalisar wakilai,"
'Yar majalisar ta bayyana cewa dokar Amurka ta yi tanadi kan tsige shugaban da ya saba kundin tsarin mulkin kasar.
Ilhan Omar ta ce:
"Dole ne a duba yiwuwar amfani da Sashe na 25 da kuma tsige shi, ya kamata Majalisa ta kuma dauki mataki kan dokar ikon yaki domin dakatar da Trump."

Source: Facebook
Lamarin kasar Cuba zai iya taba Trump
Baya ga batun Iran, Ilhan Omar ta caccaki Donald Trump kan cewa yana musguna wa fararen hula a kasar Cuba kan takunkumin man fetur da ya kakaba.
Ta ce:
"Takunkumin man fetur da Trump ya kakaba wa Cuba na mummunan tasiri a kasar baki daya."
"Wannan yunkuri ne na mulkin danniya da neman canza gwamnati, kuma fararen hula ne ke shan wahala."
Isra'ila ta karya sharadin sulhu da Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa Firaministan Isra'ila ya rusa wani sharadi daga cikin sharudan sulhu da aka yi da Iran.
Benjamin Netanyahu ta ya yi ikirarin cewa yarjejeniyar da aka yi da Iran bata shafi daina kai hare-hare zuwa kasar Lebanon ba.
Sai dai a bayanin da Firaministan Pakistan ya yi, ya tabbatar da cewa Donald Trump ya amince da daina kai hari Lebanon a cikin yarjejeniyar.
Asali: Legit.ng


