Amurka da Isra'ila Sun Kara Tsokano Fada, Sun Farmaki Muhimman Waje a Iran

Amurka da Isra'ila Sun Kara Tsokano Fada, Sun Farmaki Muhimman Waje a Iran

  • Yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sake daukar zafi
  • A ranar Talata, 7 ga watan Afirilun 2026 an kai farmaki kan tsibirin Kharg wanda yake da matukar muhimmanci ga Iran
  • Kai farmakin dai na zuwa ne yayin da wa'adin da Donald Trump ya ba kasar Iran kan bude mashigar Hormuz ke dab da karewa

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - An kai hare-hare da dama a tsibirin Kharg na ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Wannan tsibiri shi ne babban cibiyar fitar da danyen man fetur na ƙasar Iran.

An kai hari a tsibirin Kharg na Iran
Tsibirin Kharg na jamhuriyar Musulunci ta Iran Hoto: Atta Kenare
Source: Getty Images

Tashar Sky News ta kawo rahoton kai hare-hare a tsibirin na Kharga a ranar Talata, 7 ga watan Maris 2026.

Rahoton tashar CNN ya nuna cewa an ji karar fashe-fashe da dama sakamakon hare-haren da aka kai a tsibirin na Kharg.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Iran ta sha alwashi kan Amurka da Isra'ila ana shirin tsagaita wuta

Amurka ta riga ta kai wa tsibirin Kharg hari a farkon yaƙin, amma a lokacin Donald Trump ya jaddada cewa sun ƙyale muhimman wuraren man fetur ɗin Iran ba tare da taɓa su ba.

Sai dai kuma, Trump ya sha yin barazanar cewa Amurka na iya ƙwace tsibirin domin ta mallaki man fetur ɗin Iran.

Karin bayani kan tsibirin Kharg na Iran

Tsibirin na Kharg, wanda tsawonsa ya kai mil biyar, shi ne wurin da ake fitar da fiye da kashi 90 na man fetur ɗin Iran da ake sayarwa a ƙasashen waje.

A shekarun 1950 ne aka mayar da tsibirin Kharg ya zama babban rumbun adana man fetur kamar yadda yake a yau.

Tsibirin Kharg gida ne ga aƙalla mazauna 8,000, waɗanda akasarinsu ma'aikatan mai ne.

Shiga tsibirin yana da matuƙar wahala da tsauraran matakai, wanda hakan ya sa ake yi masa laƙabi da "tsibirin da aka haramta".

Donald Trump na son kwace man Iran

Jiya Litinin, Trump ya sake nanata muradinsa kan man fetur ɗin na Iran.

"Da a ce ni ne zan zaɓa, da zan riƙe man fetur ɗin. Amma kuma ina so na faranta wa mutanen ƙasarmu rai."

Kara karanta wannan

Babu sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a garuruwa 12 na kasar Musulunci

- Donald Trump

An kai hare-hare a tsibirin Kharg na kasar Iran
Manyan jiragen ruwa na daukar mai a tsibirin Kharg na Iran Hoto: Dean Conger
Source: Getty Images

Sai dai kalaman nasa sun nuna kamar yana karkata ne ga bin ra'ayin jama'ar Amurka game da yaƙin.

Trump ya ƙara da cewa:

"Abin takaici, jama'ar Amurka za su so ganin mun dawo gida. Da a ce a hannuna abin yake, da na kwashe man fetur ɗin, da na riƙe shi, domin zai kawo kuɗi masu yawa. Kuma zan kula da mutanen Iran fiye da yadda aka kula da su a baya."

Trump ya bayyana mamakinsa kan Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana mamakin da ya yi kan Iran a yakin da ake gwabzawa.

Shugaba Trump ya bayyana cewa yadda Iraniyawa ke rokon Amurka ta ci gaba da jefa masu bama-bamai a kusa da gidajen da suke zaune, ya yi matukar ba shi mamaki.

Donald Trump ya ce abin mamaki ne matuka yadda wasu daga cikin ‘yan Iran ke nuna kamar ba su damu da hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai wa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng