Mojtaba Khamenei Ya Fadi Abin da ba Zai Sare Gwiwoyin Sojojin Iran ba
- Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi magana kan kisan da Isra'ila da Amurka ke yi wa kwamandojin kasarsa
- Mojtaba Khamenei ya bayyana cewa dakarun sojojin Iran ba za su karaya ba kan abin da makiyan kasar ke aikata wa shugabanninsu
- Jagoran addinin na Iran ya yi martani ne kan kisan baya-bayan nan da Isra'ila ta yi wa babban jami'in leken asiri na rundunar IRGC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi magana kan kisan da Amurka da Isra'ila ke yi wa kwamandojin sojojin Iran.
Mojtaba Khamenei ya bayyana cewa dakarun sojojin Iran ba za su tsorata ba sakamakon kisan kwamandojinsu.

Source: Getty Images
Tashar CNN ta kawo rahoton cewa Mojtaba Khamenei ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilun 2026.
Mojtaba ya yi martani kan kisan Khademi
Kalamansa na zuwa ne biyo bayan kisan babban jami’in leƙen asirin dakarun juyin juya hali na Iran, Manjo Janar Majid Khademi, a safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Afrilun 2026.
"Khademi ya kwashe shekaru da dama yana hidima cikin natsuwa da sadaukarwa a fannonin tsaro, leƙen asiri, da kare ƙasa."
“Duk da haka, sahu-sahu na mayaka da ke kan tafarkin gaskiya a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da dakarun tsaro masu sadaukarwa, sun kafa wani gagarumin shinge mai tushe wanda ta’addanci da aikata laifuffuka ba za su taba iya raunana aniyarsu ta kishin jihadi ba."
- Mojtaba Khamenei
Jaridar The Times of Israel ta ce wadannan kalaman na Khamenei sun fito ne a cikin wata sanarwa ta rubutu. Ba a sake ganinsa a bainar jama'a ba tun bayan da ya gaji mahaifinsa, Ali Khamenei, wanda aka kashe a farkon yaƙin.
Isra'ila na kashe manyan jami'ai a Iran

Kara karanta wannan
Kasar Musulunci ta yi rashi: Isra'ila ta kashe shugaban hukumar leken asirin Iran
Tun bayan ɓallewar rikicin a ƙarshen watan Fabrairu, Isra'ila ta farmaki manyan jami'an siyasa da na soja na Iran da dama.
Mahukunta a Tehran da kuma Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, duk sun tabbatar da kisan Khademi.

Source: Twitter
Katz ya bayyana cewa Khademi “shi ne ke da alhakin kai-tsaye” na mutuwar fararen hular Isra’ila “kuma yana ɗaya daga cikin manyan mutane uku” a cikin dakarun juyin juya hali (IRGC).
Har ila yau, a ranar Litinin, dakarun Isra'ila sun bayyana cewa dakarunsu na sama sun “kashe” Asghar Bagheri, kwamandan sashen ayyuka na musamman na rundunar Quds tun shekarar 2019.
Tehran ba ta yi sharhi kan wannan iƙirarin ba.
Martanin Iran kan barazanar Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta yi martani kan barazanar da Donald Trump ya yi ta farmakar tashoshin lantarkin kasar.
Rundunar IRGC ta bayyana barazanar Donald Trump na tarwatsa ƙasar a matsayin "marar tushe" kuma ta lashi takobin ci gaba da fafatawa.
Ta kuma sha alwashin mayar da martani mai zafi idan har aka yi gigin farmakar wuraren da suka shafi fararen hula a kasar.
Asali: Legit.ng
