Iran Ta Yi Martani kan Barazanar Trump, Ta Fadi Matakin da Za Ta Dauka

Iran Ta Yi Martani kan Barazanar Trump, Ta Fadi Matakin da Za Ta Dauka

  • Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta tanka bayan da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi wata barazana
  • IRGC ta bayyana cewa barazanar Donald Trump ba za ta taba sanya wa gwiwoyinta su sare ba wajen ci gaba da fafata wa
  • Martanin rundunar na zuwa ne bayan da Trump ya yi barazanar kai farmaki kan tasoshin lantarkin Iran idan ba ta bude mashigar Hormuz ba

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi martani kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi.

Rundunar IRGC ta bayyana barazanar Donald Trump na tarwatsa ƙasar a matsayin "marar tushe" kuma ta lashi takobin ci gaba da fafatawa.

Iran ta yi martani kan barazanar Trump
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Andrew Caballero-Reynolds, Reza B
Source: Getty Images

Tashar CNN ta ce kakakin hedkwatar tsaro ta Khatam al-Anbiya ta IRGC, Laftanar Kanal Ebrahim Zolfaqari, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 7 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Iran ta sha alwashi kan Amurka da Isra'ila ana shirin tsagaita wuta

Wane martani Iran ta yi kan barazanar Trump?

Ebrahim Zolfaqari ya bayyana cewa barazanar ta Trump ba za ta dakatar da Iran daga fafatawa ba, tashar Press tv ta dauko rahoton.

"Kalaman rashin kunya, girman kai da barazana marasa tushe na shugaban Amurka mai raki, waɗanda suka samo asali daga halin ƙuncin da yake fuskanta da kuma nufin ba da hujja ga yawan kayen da sojojin Amurka suke sha ba za su dakatar da Iran daga fafatawa ba."
"Idan har aka sake kai hare-hare kan wuraren da ba na farar hula ba, martaninmu na ramuwar gayya zai kasance mafi ƙarfi kuma a babban sikelin da ya fi baya."
"An wulaƙanta Amurka a Yammacin Asiya."

- Ebrahim Zolfaqari

Iran ta kunyata Amurka

Kakakin ya ƙara da cewa barazana ba za ta iya goge kunyar da Amurka ta fuskanta a Yammacin Asiya ba.

Trump ya yi barazanar kai hari kan tasoshin wutar lantarki na Iran, gadoji, da sauran ababen more rayuwa idan har Tehran ba ta amince da buƙatun Amurka ba.

Kara karanta wannan

Iran ta yi wa Isra'ila babbar llla a mashigar Hormuz bayan babbake jirgin ruwanta

Washington ta kuma bayar da shawarar yiwuwar kai farmaki ta ƙasa.

Trump na yi wa Iran barazana

Trump ya sha yin gargaɗin cewa Amurka za ta iya kai hari kan tasoshin wutar lantarki, gadoji da sauran ababen more rayuwa a Iran idan har Tehran ta gaza kulla yarjejeniya ko kuma sake buɗe Mashigar Hormuz, wacce hanya ce mai matuƙar muhimmanci ga jigilar man fetur.

Trump na yi wa Iran barazana
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

A wani taron manema labarai ranar Litinin, ya ce ana iya "kakkabe" Iran a dare ɗaya kuma ya ce hakan "yana iya" faruwa a yammacin Talata.

Ya riga ya bayyana cewa Iran tana da lokaci har zuwa ƙarfe 8:00 na daren Talata don ƙulla yarjejeniya.

Trump ya fadi abin da yake so daga Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana abin da yake son samu daga kasar Iran.

Trump ya sanar da duniya cewa idan da za a ba shi zabi, zai so ya kwace danyen mai na kasar Iran gaba daya ya koma karkashin ikon kasar Amurka.

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa idan aka ba shi zabi, zai kwashe danyen man fetur din Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng