Ana Sabon Shirin Kawo Karshen Yakin Iran, ana Son Tsagaita Wuta na Wasu Kwanaki

Ana Sabon Shirin Kawo Karshen Yakin Iran, ana Son Tsagaita Wuta na Wasu Kwanaki

  • Wasu kasashe da ke shiga tsakani suna tattaunawa kan sharudan yiwuwar tsagaita wuta na kwanaki 45 a yakin da ake tsakanin Amurka da Iran
  • An bayyana cewa ana fatan tsagaita wutar ya iya kai wa ga kawo karshen yaki gaba daya, kamar yadda wata majiya ta ce a ranar Lahadi
  • Rahotanni sun sanar da cewa majiyoyi hudu daga Amurka, Isra’ila da yankin Gabas ta Tsakiya da ke da masaniya kan tattaunawar ne suka yi bayani

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Amurka, Iran da masu shiga tsakani suna tattaunawa kan sharudan yiwuwar tsagaita wuta na kwanaki 45 wanda zai iya kaiwa ga kawo karshen yakin da ake gaba daya.

Hakan na zuwa ne bayan shafe sama da wata guda ana bata kashi tsakanin dakarun Amurka/Isra'ila da Iran, lamarin da ya jawo mutuwar sojoji da fararen hula.

Kara karanta wannan

Amurka ta ji wuta, Trump ya nemi a tsagaita wuta a yakin da ake yi da Iran

Mojtaba Khamenei da Donald Trump
Mojtaba Khamenei a hagu, Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Kokarin tsayar da yakin Iran

Yayin da aka fara maganar sulhu, wasu majiyoyi sun shaidawa kafar labarai ta Axios cewa damar cimma yarjejeniya ta wucin gadi cikin sa’o’i 48 masu zuwa ba ta da yawa.

An sanar da cewa wannan kokari ne kadai damar da za ta iya hana tsananta rikicin da zai jawo manyan hare-hare kan muhimman abubuwan more rayuwa na fararen hula a Iran da kuma ramuwar gayya a kasashen Larabawa.

Trump ya shaida cewa Amurka na cikin tattaunawa da Iran, kuma ana iya cimma yarjejeniya kafin wa’adin ya kare a ranar Talata.

Reuters ta rahoto Trump ya ce:

“Abubuwa na tafiya da kyau, amma idan ba su kulla yarjejeniya ba, zan rusa komai a can,”

Yadda ake tattauna batun yakin

Majiyoyi hudu da ke da masaniya kan kokarin diflomasiyya sun ce ana gudanar da tattaunawar ta hannun masu shiga tsakani daga Pakistan, Masar da Turkiyya.

Kara karanta wannan

'Ba da mu ba': Iran ta sake gindaya sharudan tsagaita wuta a yaki da Isra'ila

Haka kuma majiyar ta ce ana tattaunawa ta sakonnin rubutu tsakanin wakilin Trump, Steve Witkoff, da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi.

Wani jami’in Amurka ya ce gwamnatin Trump ta gabatar wa Iran da shawarwari da dama a kwanakin baya, amma har yanzu jami’an Iran ba su amince da su ba.

Majiyoyin sun ce masu shiga tsakani na tattaunawa kan yarjejeniya mai matakai biyu; mataki na farko zai kasance tsagaita wuta na kwanaki 45 inda za a tattauna yadda za a kawo karshen yaki gaba daya.

Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu na bayani a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahotannin da suka fito sun bayyana cewa mataki na biyu zai kasance yarjejeniya ta karshe kan kawo karshen yakin da ya jawo asarar rayuka da dukiya mai tarin yawa.

Yakin Iran: Sojan Amurka ya magantu

A wani labarin, kun ji cewa wani sojan Amurka dan asalin Najeriya daga jihar Kano ya yi tsokaci kan wani farmaki da sojoji suka kai Iran.

Suleiman Isah Isah ya sanar da cewa Amurka tana kokari wajen kubutar da sojojinta da suka shiga matsala a fagen fama ba kamar wasu kasashe ba.

Ya bayyana haka yayin da 'yan Najeriya ke ta magana kan yadda aka lalata wasu jiragen yakin Amurka a kasar Iran yayin aikin ceto wani soja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng