An Sake Taso Shugaba Trump, Sojojin Amurka na cikin Hadari a Yaki da Kasar Iran

An Sake Taso Shugaba Trump, Sojojin Amurka na cikin Hadari a Yaki da Kasar Iran

  • Shugaba Donald Trump na kokarin jefa rayuwar sojojin Amurka cikin babban hadari a yakin da yake da kasar Musulunci ta Iran
  • Dan Majallisar Amurka na jam'iyyar Democrat, Seth Moulton ne ya bayyana hakan da yake martani ga jawabin da Trump ya yi
  • Tsohon sojan ya bayyana cewa kalaman Trump na cin karo da juna, kuma ya fahimci shugaban kasar bai ma san abin da yake yi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Wasu manyan ’yan majalisar Amurka na jam’iyyar Democrat na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan dabarun Shugaba Donald Trump a yakinsa da kasar Iran.

Dan Majalisa Seth Moulton, wanda tsohon sojan ruwa ne, ya bayyana cewa tsarin Shugaba Trump na "rashin sani" game da Iran ya jefa rayukan sojojin Amurka cikin yanayi na "haɗari."

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na gaisawa da wasu dakarun sojoji Hoto: U.S Army
Source: Twitter

Dan Majalisa ya dura kan Shugaba Trump

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito tsohon sojan na Amurka na cewa tun farkon yakin zuwa yanzu, Trump ya gaza cimma manufofin da ya sanya gaba.

“Shugaba Trump ba shi da hankali domin ya tsufa kuma yana yawan gyangyaɗi. A gaskiya ma, jawabin da ya yi kan yakin Amurka da Iran abin tausayi ne wanda ya nuna yadda yake da rauni da jahilci.
"Abin zai zama kamar wasan kwaikwayo ne idan ba don muhimmancin lamarin ba, amma lamarin yana da matuƙar muhimmanci, kuma shi ya sa hakan yake da haɗari a gare mu da kuma sojojinmu,” in ji Moulton.

Yadda kalaman Trump ke karo da juna

Ɗan majalisar ya yi nuni da cewa Trump ya yi "fankama wajen soke yarjejeniyar Obama" alhalin kuma yana ƙoƙarin samun wata yarjejeniya, lamarin da ya kira tufka da warwara.

Moulton ya kara da cewa bayan haka, ya ce "canjin gwamnatin Iran ba ya cikin tsarinsa" alhalin kuma yana kiran al'ummar Iran su tashi su sauya gwamnatinsu, in ji NBC News.

Kara karanta wannan

Trump ya gamu da matsala a Amurka, kotu ta tsayar da aikin $400m ana yakin Iran

Moulton ya ƙara da cewa a zahiri ma Trump ya samu canjin gwamnatin a Iran, amma ba ta hanyar da yake so ba:

"Ya maye gurbin tsoho mai shekaru 86 wanda ba shi da wata lafiya da wani mutum mai kuzari da ke ganiyarsa a shekaru 50, wanda kuma ya fi tsohon tsauri. Saboda haka, wannan canjin gwamnati ne ta kishiyar hanyar da muke buƙata."
Seth Moulton.
Dan Majalisar dokokin Amurka na jam'iyyar Democrat, Seth Moulton Hoto: Anadolu
Source: Facebook

Haka kuma, Moulton ya soki ikirarin Trump na cewa ya "ruguje shirin nukiliyar Iran watanni kalilan da suka gabata," amma yanzu kuma yana cewa sai an sake kai musu hare-hate na wasu makonni biyu zuwa uku.

A ƙarshe, Moulton ya kammala da cewa:

“Ni ba masanin halayyar yara ba ne, don haka ba zan iya fahimtar abin da ke cikin zuciyar Donald Trump ba.”

Iran ta karbi bukatun tsagaita wuta

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Musulunci ta Iran ta gabbatar da cewa ta karbi sakon neman tsagaita wuta a yakin da take yi da kasashen Amurka da Isra'ila.

Kakakin Ma’aikatar Wajen ƙasar Iran, Esmaeil Baghaei, ne ya bayyana hakan, yana mai tabbatar da cewa masu shiga tsakani sun mika wa kasar bukatu.

Tun farko dai Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya musanta rade-radin cewa sun hau teburin tattaunawa da Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262