Rigima Sabuwa: Trump Ya Jefawa Mataimakinsa Zargi kan Yakin Iran

Rigima Sabuwa: Trump Ya Jefawa Mataimakinsa Zargi kan Yakin Iran

  • Shugaban Amurka ya gabatar da wani jawabi na musamman game da yakin da suka hada kai da Isra'ila suka kaddamar a kan Iran
  • Yayin da ya ke yawan maimaita batun sulhu, shugaba Donald Trump ya yi wasu kalamai da suka nuna zargi ga mataimakinsa, JD Vance
  • A nata bangaren, Iran ta nuna cewa dole duk wani sulhu da za a yi ya jawo daina kai mata hari gaba daya ba wai kawai tsagaita wuta ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa shi za a yabawa idan tattaunawa da Iran kan tsayar da yaki ta yi nasara.

A lokacin da ya yi bayanin, Donald trump ya yi kalamai da suka nuna cewa bai kamata a zarge shi ba idan aka gagara daidaitawa.

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

Shugaba Donald Trump da JD Vance
Donald Trump da mataimakinsa a fadar White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wall Street Journal ta wallafa cewa Trump ya faɗi hakan ne yayin liyafar Easter a Fadar White House, a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da Iran domin tsagaita wuta a rikicin da ya shiga mako na biyar.

Iran: Trump ya zargi mataimakinsa

A cikin wani bidiyo daga taron da ya bayyana a yanar gizo, an ga Trump yana tambayar Vance kan yadda tattaunawar da ya ce ana yi da Iran ke tafiya.

Ana haka ne Donald Trump ya ce idan an cimma yarjejeniya, shi za a yabawa gaba ɗaya, amma idan aka samu matsala, Vance za a zarga.

“Idan yarjejeniyar Iran ba ta yi nasara ba, zan ɗaura laifi kan JD Vance. Idan kuma ta yi nasara, ni za a yabawa,”

Inji Trump

A baya, wani rahoto ya bayyana cewa Iran ta fi son tattaunawa da Vance maimakon wakili na musamman, Steve Witkoff, surukin Trump, Jared Kushner, da kuma ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio.

Kara karanta wannan

A karshe, Trump zai hakura da yakin Iran ko ba yarjejeniya, ya saka lokaci

Matsayar Iran kan sulhu da Amurka

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran ya fitar da sanarwa a matsayin martani ga kalaman Trump, inda shugaban Amurka ya yi barazanar cewa dole Iran ta amince da yarjejeniya cikin makonni biyu zuwa uku.

“Ba za mu yarda da wannan ba, tattaunawa, tsagaita wuta, sannan a sake komawa yaki ba,”

Inji Esmail Baghaei, yana mai bayyana rikicin a matsayin matsala ce ga yankin baki ɗaya da kasashen duniya ba Iran kawai ba.

Jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei
Mojtaba Khamenei da ke jagorantar Iran a yanzu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Baghaei ya ce Iran za ta ci gaba da mayar da martani matuƙar hare-haren Amurka da Isra’ila na ci gaba, tare da jaddada cewa Tehran ba ta ɗaukar ƙasashen yankin Gulf a matsayin abokan gaba.

Al-Jazeera ta rahoto ya ce:

“Mun sha faɗa cewa muna da niyyar ci gaba da kyakkyawar mu’amala da makwabtanmu. Matsalar ita ce Amurka da Isra’ila suna amfani da ƙasashensu wajen kai hare-hare kan Iran,”

Amurka ta tsara shiga Iran

Kara karanta wannan

Abu ya gagara: Trump zai janye yaki da Iran ba tare da bude Hormuz ba

A wani labarin, mun kawo muku cewa sojojin Amurka sun gabatarwa shugaba Donald Trump shirin shiga Iran da sojoji da kayan tono sinadarin uranium.

Hakan na zuwa ne bayan Trump ya sha alwashin rusa duk wani shiri da Iran ta domin mallakar makamin nukiliya da ya ce barazana ne ga Amurka.

Wani tsohon sojan Amurka ya bayyana cewa za a bukaci dubban sojoji, kayan aiki na musamman kuma za a dauki lokaci kafin shirin ya yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng