Iran Ta Jefa Babban Rikici tsakanin Trump da Kasashen Turai kan NATO
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa kasashen Turai barazana game da kungiyar tsaro ta NATO da suka kafa tun a shekarar 1949
- Hakan na zuwa ne bayan kasashen sun ki taimaka masa wajen bude mashigar Hormuz da Iran ta toshe saboda yakin da Amurka ta fara
- Rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi ya jawo tashin farashin man fetur da gas a fadin duniya, lamarin da ya shafi tattalin arzikin kasashe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Bayan shafe shekara 77 suna tare da juna, shugaba Donald Trump ya bayyana cewa yana shirin raba hanya da kasashen Turai.
Ya bayyana haka ne inda ya yi barazanar fita daga kungiyar NATO da Amurka ta hada kai da Turawan Yamma suka kafa a shekarar 1949.

Source: Facebook
Donald Trump zai cire Amurka daga NATO
Donald Trump ya shaida wa jaridar the Telegraph cewa yana matuƙar tunanin fitar da Amurka daga ƙungiyar NATO bayan ta kasa shiga yaƙin da yake yi da Iran.
Shugaban ya bayyana ƙungiyar a matsayin mai rauni, yana mai cewa cire Amurka daga yarjejeniyar tsaro yanzu ya wuce batun sake tunani.
Wannan ne mafi ƙarfi daga cikin alamomin da ke nuna cewa Fadar White House ba ta ganin Turai a matsayin amintacciyar abokiyar hulɗa, bayan ƙasashen sun ƙi amsa buƙatar Trump na tura jiragen yaƙi don buɗe mashigar Hormuz.
Lokacin da aka tambaye shi ko zai sake nazarin kasancewar Amurka a NATO bayan rikicin, Al-Jazeera ta rahoto Trump ya amsa cewa:
“Eh, zan ce ya wuce a sake tunani. Ban taɓa dogaro da NATO ba. Tun farko na san cewa ƙungiyar mai rauni ce, kuma Putin ma ya san hakan.”
Laifin kasashen Turai a wajen Trump
Ƙasashen NATO sun nuna ƙin shiga aikin buɗe mashigar ruwan Hormuz, wadda kusan kashi 20 cikin 100 na man duniya ke wucewa ta cikinta.

Source: Getty Images
Iran ta rufe mashigar tsawon makonni, lamarin da ya haifar da hauhawar farashin mai da iskar gas a duniya tare da barazanar jefa tattalin arzikin duniya cikin koma baya.
Trump ya ce ya sha mamaki
Trump ya nuna cewa rashin shiga bude mashigar Hormuz ya ba shi mamaki lura da yadda Amurka ke tallafawa kasashen NATO.
Ya ce:
“Abin ma ya ba ni mamaki. Ban matsa musu lamba sosai ba, kawai na ce, ‘to’, amma ina ganin ya kamata hakan ya kasance kai tsaye.”
“Mu mun kasancewa a shirye ko yaushe, har da Ukraine. Mun kasance tare da su. Amma su ba su kasance tare da mu ba.”
Shugaba Trump zai bar yakin Iran
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa Donald Trump ya bayyana cewa nan gaba kadan zai janye daga yakin da ya kaddamar a Iran.
Trump ya sanar da cewa ya gama mafi wahala daga cikin yakin, saboda haka zai tattara kayansa ya yi gaba ko ba a bude Hormuz ba.
Shugaban Amurka ya kara da cewa zai fita daga yakin ne ko ba a cimma wata yarjejeniya da Iran ba nan da mako biyu zuwa uku masu zuwa.
Asali: Legit.ng


