Yaki Ya Yi Zafi; Iran Ta Farmaki Sojojin Amurka 500, an Ji Abin da Ya Faru
- Dakarun sojojin Iran sun yi ikirarin kai famaki kan sojojin Amurka yayin da yaki ke kara zafi a yankin Gabas ta Tsakiya
- Babbar hedkwatar Khatam al-Anbiya ta bayyana an farmaki sojojin 500 a wurare daban-daban da suka boye a Dubai, inda aka kashe da dama daga cikinsu
- Rundunar Centcom ta sojojin Amurka ta yi martani kan ikirarin na sojojin Iran dangane da kai harin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Babbar hedkwatar Khatam al-Anbiya ta sojojin Iran ta ce ta farmaki dakarun Amurka sama da 500.
Ta bayyana cewa an farmaki dakarun ne a sabon farmakin da sojojin Iran suka kai, wanda ya janyo musu "asarar dukiya da rayuka masu yawa."

Source: Twitter
A cewar rahoton tashar Press tv ta Iran, kakakin hedikwatar, Laftanar Kanal Ebrahim Zolfaqari, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 28 ga watan Maris 2026.
Iran ta farmaki sojojin Amurka
Ya bayyana cewa dakarun Amurka sun tsere daga sansanoninsu na yankin sakamakon "munanan hare-hare" kuma suna fakewa a wasu wurare biyu da ba sansanoninsu ba ne.
A cewar sanarwar, maboya ta farko a Dubai tana ɗauke da ma'aikata sama da 400, yayin da ta biyu kuma tana ɗauke da fiye da 100.
Dakarun sojojin sama da na ruwa na rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) ne suka farmaki wuraren biyu da makamai masu linzami masu saiti da jirage marasa matuƙa.
Kakakin ya bayyana hare-haren a matsayin waɗanda suka janyo "asarar rayuka masu yawa" sannan ya ce motocin ɗaukar marasa lafiya sun kwashe sa'o'i suna jigilar sojojin Amurka, har da kwamandoji.
An ja kunnen Donald Trump
Haka zalika, sanarwar ta yi gargaɗi ga shugaban Amurka Donald Trump da kwamandojin sojin Amurka cewa yankin zai zama "makabartar sojojin Amurka" sannan ta jaddada cewa zaɓi ɗaya tilo da suke da shi shi ne mika wuya.

Kara karanta wannan
Iran ta gano masu ba sojojin Amurka mafaka, ta sha alwashin ruguza su da hare hare
A wata sanarwar ta daban, kakakin ya bayyana cewa a sanyin safiyar Asabar, dakarun sojojin Iran sun harbi wani jirgin ruwa na sojojin Amurka a wani wuri mai nisa daga tashar jiragen ruwa ta Salalah da ke Oman.
Sanarwar ta jaddada cewa Iran tana girmama ikon ƙasar Oman, wadda ta bayyana a matsayin ƙasa ’yar’uwa kuma abokiya.

Source: Facebook
Amurka ta musanta harin
Rundunar Centcom ta Amurka ta musanta cewa Iran ta farmaki dakarunta a Dubai.
A wani rubutu a shafinta na X, rundunar ta bayyana cewa:
"Babu wani ma'aikacin Amurka da aka kai wa hari a Dubai. Gwamnatin Iran na ƙirƙirar ƙaryace-ƙaryace a shafukan sada zumunta ne domin ɓoye gaskiyar cewa ƙarfin sojinsu ya raunana kuma an ragargaje su."
Iran ta kai hare-hare masu zafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta kaddamar farmaki rukuni na 83 na hare-haren ramuwar gayya da ta sanya wa sunan "Operation True Promise 4"
Rundunar IRGC ta bayyana cewa farmaki muhimman cibiyoyin soja na Amurka da Isra'ila a faɗin yankin da makamai masu linzami da jirage marasa matuka.
IRGC ta farmaki sansanonin sojojin Amurka na Al-Dhafra da Al-Udeiri, tare da rumbunan gyara da adana jiragen sufuri da jirage marasa matuka a sansanin sama na Ali Al-Salem.
Asali: Legit.ng
