Sojojin Isra'ila Sun Sha Kashi, Mayakan Hezbollah Sun Samu Nasara a Kansu

Sojojin Isra'ila Sun Sha Kashi, Mayakan Hezbollah Sun Samu Nasara a Kansu

  • Mayakan kungiyar Hezbollah na fafatawa da dakarun sojojin Isra'ila da suka shigo Kudancin Lebanon a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Dakarun sojojin Isra'ila sun ji ba dadi a hannun mayakan Hezbollah yayin da fafatawa ke kara zafi a tsakanin bangarorin biyu
  • Mayakan na Hezbollah sun harba rokoki kan sojojin Isra'ila inda suka samu nasarar illata wasu daga cikinsu

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Beirut, Lebanon - Mayakan Hezbollah na ci gaba da gwabza fada da dakarun sojojin Isra'ila a Kudancin Lebanon.

Sojojin Isra'ila tara, ciki har da jami'ai biyu, sun jikkata a hare-haren rokoki guda biyu da mayakan Hezbollah suka harbo daga Kudancin Lebanon.

Mayakan Hezbollah sun kashe sojojin Isra'ila
Sojojin Isra'ila dauke da makamai Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton jikkata sojojin na Isra'ila da mayakan Hezbollah suka yi a ranar Asabar, 28 ga watan Maris 2026.

'Yan Hezbollah sun raunata sojojin Isra'ila

Kara karanta wannan

Sojojin Isra'ila sun sha azaba a hannun mayakan Hezbollah, an ji abin da ya faru

Majiyoyi sun bayyana cewa sojoji bakwai da jami'ai biyu ne suka jikkata, ba tare da fayyace ko raunukan sun faru ne sakamakon harin roka na kai-tsaye ko kuwa lokacin da aka kakkabo rokokin ba.

Mai magana da yawun rundunar sojoji, Yedioth Ahronoth ya bayyana cewa wani jami'i ya ji rauni mai tsanani yayin da wani kuma ya ji rauni matsakaici bayan an harba makamin fasa tankoki daga Kudancin Lebanon.

Kakakin ya ƙara da cewa a wani lamari na daban a daren jiya, wani jami'in ya ji rauni mai tsanani, tare da sojoji shida da suka samu raunuka matsakaici a harbin rokoki daga Kudancin Lebanon, rahoton tashar Anadolu Ajansi ya tabbatar da hakan.

Hezbollah na fafata wa da sojojin Isra'ila

Hakan na zuwa ne yayin da sojojin Isra'ila ke ƙara kutsa kai cikin yankin Lebanon, inda suka ci gaba da tafiya har tsawon kilomita 7 (mil 4.3) a wasu yankunan.

Yayin da sanarwar rundunar sojojin ba ta fayyace inda aka kai hare-haren ba, ta zo sa'o'i kaɗan bayan da aka ce Hezbollah ta yi wa dakarun Isra'ila kwanton ɓauna a garin Taybeh da ke Kudancin ƙasar, kimanin kilomita 6 (mil 3.7) daga kan iyaka.

Kara karanta wannan

Sojoji na fifita 'yan bindiga fiye da mutanen da aka zalunta? Rundunar ta magantu

Isra'ila na kai hare-hare a Lebanon
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: @netanyahu
Source: Twitter

Isra'ila na kai hare-hare a Lebanon

Isra'ila ta ragargaji Lebanon da hare-haren sama tare da ƙaddamar da harin ƙasa a Kudancin ƙasar tun bayan harin da Hezbollah ta kai ta kan iyaka a ranar 2 ga Maris 2026.

A yammacin ranar Juma'a, ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila ya karu zuwa 1,142, yayin da wasu 3,315 suka jikkata.

Uganda za ta taya Isra'ila yaki da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa kasar Uganda da ke nahiyar Afrika na shirin taimakon Isra'ila kan yaki da Iran.

Babban hafsan sojin Uganda, Muhoozi Kainerugaba, ya bayyana shirinsa na yaƙi tare da Isra'ila a rikicin da take yi da Iran.

Ya yi kira da a kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa, amma ya yi gargadin cewa duk wani yunƙuri na lalata Isra’ila na iya sa Uganda ta shiga yaƙin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng