Trump Na cikin Yaki da Iran, Gagarumar Matsala Ta Tunkaro Shi a Amurka

Trump Na cikin Yaki da Iran, Gagarumar Matsala Ta Tunkaro Shi a Amurka

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na ci gaba da jagorantar yakin da kasarsa ta kaddamar kan Iran tare da hadin gwiwar Isra'ila
  • Yayin da Trump ke ci gaba da ikirarin samun gagarumar nasara a yakin da ake, matsala ta tunkaro shi a cikin gida
  • An shirya gudanar da wata gagarumar zanga-zanga domin nuna adawa da salon mulkinsa da manufofin gwamnatinsa

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Ana sa ran gudanar da gagarumar zanga-zanga a faɗin ƙasar Amurka domin nuna adawa ga Shugaba Donald Trump.

Za a yi zanga-zangar ne yayin da miliyoyin mutane ke fito da fushinsu kan abin da suke kallo a matsayin mulkin kama-karya da sauran hanyoyin cin zarafin bil'adama da take dokoki.

Za a gudanar da zanga-zangar adawa da Trump a Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa za a gudanar da zanga-zangar ne a ranar Asabar, 28 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Lissafi na neman kwacewa: Trump na son gama yaki da Iran cikin gaggawa

Za a yi zanga-zangar adawa da Trump

Wannan ne karo na uku a ƙasa da shekara guda da Amurkawa za su fito kan tituna a matsayin ɓangare na wani yunkuri na jama'a da aka yi wa laƙabi da "No Kings".

Yunkurin dai shi ne babban dandalin nuna rashin amincewa da Trump tun bayan fara wa'adin mulkinsa na biyu a watan Janairun 2025.

Kuma a yanzu suna da wani sabon dalilin yin fushi, yaƙin Iran wanda Trump ya ƙaddamar tare da Isra'ila, mai manufofi da jadawalin kammalawa da ke yawan sauyawa.

Ranar farko ta irin wannan zanga-zangar a faɗin ƙasa ta zo ne a watan Yunin 2025, ranar cikarsa shekaru 79 da haihuwa, wadda ta zo daidai da fareti na soja da ya nace sai an yi a Washington.

Miliyoyin mutane da dama ne suka fito, tun daga New York har zuwa San Francisco da sauran wurare da dama a tsakani.

Rana ta biyu ta "No Kings" a watan Oktoba ta jawo kimanin masu zanga-zanga miliyan bakwai, a cewar masu shirya taron.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: An yi wa jirgin Isra'ila ruwan wuta bayan tura shi kai hari

Meyasa za a yi zanga-zangar?

Manufar yanzu ita ce fito da mutane fiye da haka a ranar Asabar, yayin da farin jinin Trump ya ragu zuwa kusan kashi 40 cikin 100, tashar France24 ta kawo rahoton.

Sannan zaɓubbukan tsakiyar wa'adi na gabatowa a watan Nuwamba, inda jam'iyyar Republican ta Trump za ta iya rasa iko da duka rukunonin majalisar dokoki biyu.

Kamar yadda mutane da dama a ƙungiyarsa ta "Make America Great Again" ke girmama Trump, haka su ma mutanen da ke ɗayan ɓangaren siyasar Amurka ba sa ƙaunarsa.

Za a yi zanga-zangar adawa da Donald Trump
Masu zanga-zangar adawa da Trump a Amurka Hoto: Joseph Prezioso
Source: Getty Images

Abokan hamayyar Trump suna kukan yadda yake amfani da dokokin zartarwa wajen mulki, amfani da ma'aikatar shari'a wajen gurfanar da abokan hamayya.

Ana adawa da manufofin Trump

Suna kuma adawa da yaƙi da shirye-shiryen sauya jinsi, da kuma sabuwae sha'awar nuna ƙarfin sojojin Amurka bayan ya yi kamfen a matsayin mutumin da ke son zaman lafiya.

"Tun bayan zanga-zangarmu ta ƙarshe, wannan gwamnati ta jefa mu cikin yaƙi sosai," in ji Naveed Shah na ƙungiyar Common Defense, wata ƙungiyar tsofaffin soji da ke cikin rukunin "No Kings".

Kara karanta wannan

Matakin farko da alkali ya dauka a zaman shari'ar El Rufai da gwamnatin Najeriya

"A gida, mun kalli yadda aka kashe 'yan ƙasa a kan tituna ta hanyar amfani da dakarun soja. Mun ga yadda aka rarraba iyalai kuma ake tsangwamar baƙi. Dukkan waɗannan an yi su ne da sunan mutum ɗaya da ke ƙoƙarin yin mulki kamar sarki."

- Naveed Shah

Iran ta raunata sojojin Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan Amurka da Isra'ila yayin da ake gwabza fada a yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta kai wani harin ramuwar gayya kan sojojin Amurka da ke wani sansani a Saudiyya, inda ta musu ruwan makamai masu linzami.

Harin na Iran a sansanin Prince Sultan da ke Saudiyya ya jikkata sojojin Amurka 12, biyu daga cikinsu cikin mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng