Houthi da Ta Gwabza da Amurka a Baya za Ta Taya Iran Yaki, Ta Fadi Sharuda
- Bayan shafe wata daya ana gwabza fada tsakanin Iran da Isra'ila/Amurka, 'yan kungiyar Houthi da ke Yemen sun ce suna shirye su shiga fadan
- Mai magana da yawun dakarun Houthi, Yahya Saree ne ya sanar da shirin su na shiga yakin a wani bidiyo ya fitar a ranar Juma'a, 27 ga Maris, 2026
- A watan Mayun shekarar 2025 gwamnatin Amurka ta yi yarjejeniyar tsagaita wuta da Houthi bayan shafe lokaci suna gwabza fada a Gabas ta Tsakiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Yemen - Yayin da ake cigaba da kai hare-hare a kasashen Gabas ta Tsakiya saboda yakin Iran da Amurka/Isra'ila, 'yan Houthi na Yemen sun ce suna daf da shiga fadan.
Hakan na zuwa a daidai lokacin da Amurka ke yawan maganar sulhu tare da fitar da wasu sharuda 15 domin ganin an dakatar da yakin.

Kara karanta wannan
Tchiani ya tsoma baki a yakin Iran da Isra'ila, yana zargin an kulla wa Nijar makirci

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta wallafa bidiyon mai magana da yawun dakarun Houthis, Yahya Saree a shafinta na X yana magana a kan sharudan shiga yakin.
Sharudan shigar Houthi yakin Iran/Amurka
‘Yan tawayen Houthi na Yemen masu goyon bayan Iran sun ce suna shirye su shiga yaki kai tsaye idan wasu kasashe suka hada kai da Amurka da Isra’ila a yakin da suke yi da Iran.
Shardi na biyu da kungiyar Houthi ta bayar kan shiga yakin shi ne yin amfani da Tekun Red Sea wajen kai hare-haren kan Iran.
“Muna tabbatar cewa yatsunmu na kan bindiga a shirin fara yaki kai tsaye idan wasu kasashe suka taya Washington da Isra’ila yakar Iran da kawayenta, ko kuma idan aka yi amfani da Tekun Red Sea wajen kai hari kan Iran.”
Inji kakakin rundunar Houthi, Yahya Saree, a wani jawabi da ya gabatar a talabijin ranar Juma’a.
A kan sharadi na uku kuma, rahoton the Hill ya ce Saree ya ce 'yan Houthi suna shirye su dauki mataki idan abin da ya kira karin tsananta hari kan Iran ya ci gaba, amma bai fayyace irin matakin da za su dauka ba.

Kara karanta wannan
Iran ta yi babban kamu, an gano mutane da ke yada sirrinta ga makiya a yaki da Isra'ila
Alamar fadaduwar yakin Iran/Amurka
Wannan gargadi na kara yiwuwar fadada yakin a yankin, musamman ganin yadda Houthi ke da ikon kai hare-hare har wajen Yemen da kuma kawo cikas ga hanyoyin sufuri na jiragen ruwa a yankin.
Kungiyar ‘yan tawayen ta Yemen ta kwace iko da babban birnin kasar, Sanaa, da kuma yawancin yankin Arewa maso Yammacin kasar tun shekarar 2014.

Source: Getty Images
Bayan Isra’ila ta kaddamar da yaki a Gaza a watan Oktoba 2023, 'yan Houthi sun rika kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka a teku tare da kai hare-haren jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami zuwa Isra’ila.
Mayakan Houthi sun kai hare-haren suna cewa suna yin hakan ne don nuna goyon baya ga Falasdinawa da ke fuskantar hare-hare a Gaza kafin a yi yarjejeniya.
Ga bayanin da Houthi ta yi a bidiyo a kasa:
Iran ta jikkata sojojin Amurka
A wani labarin, kun ji cewa sojojin Iran sun kaddamar da hare-hare masu hadari kan wani sansanin soji da ke kasar Saudiyya a daren Juma'a.
Rahotanni sun nuna cewa makaman da Iran ta harba sun raunata akalla sojojin Amurka 12, inda wasu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.
Bayan raunata sojojin Amurka, hare-haren makamai masu linzami sun lalata wasu jiragen Amurka masu dakon mai a sansanin soji a Saudiyya.
Asali: Legit.ng
