Amurka Ta Kira Ruwa; Dakarun Iran Na Musamman Sun Shirya Aikin Bazata

Amurka Ta Kira Ruwa; Dakarun Iran Na Musamman Sun Shirya Aikin Bazata

  • Yakin da ake gwabzawa tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya na shirin daukar sabon salo
  • Dakarun sojojin Iran na musamman sun shirya gagarumin aiki kan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya yayin da yakin yake kara daukar zafi
  • Wannan shirin dai na zuwa ne yayin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yake ci gaba da hakikancewa ana tattaunawa da Iran don cimma yarjejeniya kan yakin

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Dakarun sojojin Iran sun shirya kai hare-hare kan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Manyan sojojin na Iran da suka ƙunshi dakarun runduna ta 65 ta Airborne ta rundunar sojoji, wadda aka sani da NOHED, suna shirye-shirye don kai wa Amurkawa babban hari.

Sojojin Iran za su farmaki Amurka
Dakarun sojojin Iran na gudanar da fareti Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar Press tv ta kasar Iran ta kawo rahoton a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Iara'ila ta shammaci Iran, ta hallaka babban kwamandan sojoji

Wane shiri sojojin Iran ke yi kan Amurka?

Dakarun na NOHED za su kai hare-haren a wani aikin haɗin gwiwa da dakarun musamman na Saberin na rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC).

A cewar kamfanin dillancin labarai na Mehr, bincike ya nuna cewa za a gudanar da aikin ne biyo bayan fara kashi na biyu yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran.

Dakarun sojojin na musamman na Iran sun ɗauki kyakkyawan shiri don kai wa wuraren Amurka hari "mai tsanani, cikin sauri, da raɗaɗi."

Masu tsara dabarun soja na Iran suna kallon ayyuka irin su kama jami'an Amurka, ma'aikatan soja, da manyan 'yan kasuwa a matsayin matakai mafi tasiri, suna yin ishara da abubuwan da suka faru da 'yan ƙasar Amurka a shekarun 1980.

Wadanne wurare za a kai hare-haren?

Rahoton ya ƙara da cewa fannin da waɗannan ayyukan za su iya shafa zai iya haɗawa da yankin Kurdistan na Iraki har zuwa ƙasashen Tekun Fasha ciki har da Bahrain, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Kuwait.

Kara karanta wannan

Ba sassauci: Iran ta ci gaba da luguden wuta kan Isra'ila, ta farmaki muhimman wurare

Wata majiya ta bayyana cewa an tattara fiye da mayakan Iran miliyan ɗaya don yin fito-na-fito ta ƙasa da dakarun Amurka.

Iran ta shirya ba Amurka mamaki a Gabas ta Tsakiya
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Karanta wasu labaran kan yakin Amurka, Iran

Trump ya fadi abin da Iran ke tsoro

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan batun tattaunawar da ya ce kasarsa na yi da Iran don kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya bayyana cewa musantawar da Tehran ke yi ya faru ne saboda masu tattaunawar na Iran suna tsoron kada mutanensu su kashe su.

Fadar White House ta bayyana cewa Trump a shirye yake ya dauki kwakkwaran mataki idan Iran ba ta amince da shan kashi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng