Ana Wata ga Wata: Iran Ta Karyata Trump, Ta Fadi Shirinta kan Amurka da Isra'ila
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa ya fara tattaunawa da Iran domin duba yiwuwar kawo karshen yakin da ake yi
- Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta fito ta yi watsi da ikirarin na Shugaban kasar Amurka kan batun fara tattaunawa
- Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ya bayyana abin da Iran za ta yi maimakon tattaunawa da Amurka da Isra'ila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Ma'aikatar harkokin wajen Iran, ta yi martani kan ikirarin Donald Trump na fara tattaunawa kan yakin da ake yi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei ya yi watsi da iƙirarin baya-bayan nan na shugaban kasar na Amurka.

Source: Twitter
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi.
Iran ta musanta batun tattaunawa da Amurka
“Mun bayyana a jiya cewa babu wata tattaunawa ko sulhu tsakanin Iran da Amurka. Ya kamata na ce, mun fuskanci wani mummunan yanayi game da diflomasiyyar Amurka."
"An kai mana hari har sau biyu a tsakanin watanni tara a daidai lokacin da muke tsaka da tattaunawa don magance batun nukiliya. Don haka, wannan ya kasance yaudarar diflomasiyya ce.”
- Esmaeil Baghaei
Wane shiri Iran ke da shi?
Ya bayyana cewa ƙasashe da dama sun tuntuɓi Iran, suna bayar da gudunmuwar shiga tsakani da Amurka, tashar DW ta kawo labarin.
“An riƙa aika saƙonni kwanaki da dama. Mun ba da amsa ga waɗancan saƙonni. Saƙonmu a bayyane yake. Za mu ci gaba da kare kanmu."
Esmaeil Baghaei ya ƙara da cewa iƙirarin Amurka na neman tattaunawa ba abin yarda ba ne.
“Duba gaskiyar lamarin. Iran tana ƙarƙashin luguden bama-bamai da makamai masu linzami akai-akai daga Amurka da Isra'ila."
"Saboda haka, iƙirarin su na diflomasiyya da shiga tsakani ba abin yarda ba ne. Domin su ne suka fara wannan yaƙin kuma suna ci gaba da kai wa Iran hari. Don haka, shin akwai wanda zai yarda cewa iƙirarinsu na tattauna abin amincewa ne?"

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Iran ta yi martani kan ikirarin Trump na fara tattaunawa kan yakin da ake yi
- Esmaeil Baghaei
Kasashe na son shiga tsakani
Lokacin da aka tambaye shi game da rawar da Pakistan take takawa, Esmaeil Baghaei ya ce Iran ta yi amanna cewa Islamabad tana da “kyakkyawar niyya”.

Source: Twitter
Ya kuma ce Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi yana tuntuɓar takwaransa na Pakistan da kuma jami’an diflomasiyya a sauran ƙasashe.
“Don haka irin waɗannan tattaunawar suna gudana tsakanin Iran da maƙwabtanta da sauran ƙasashe abokai."
"Mun fahimci cewa ƙasashen yankin, ƙasashe maƙwabta, suna damuwa game da abubuwan da ka iya faruwa, kuma kowa yana ƙoƙarin taimakawa ta yadda yanayin zai dawo cikin kwanciyar hankali."
- Esmaeil Baghaei
Iran ta kai sababbin hare-hare
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta kasar Iran ta kaddamar da rukuni na 80 na hare-haren ramuwar gayya kan Amurka da Isra'ila.
Rundunar ta kai hari kan wasu muhimman wurare da cibiyoyin sojoji a yankin Arewacin Isra'ila, baya ga luguden wuta kan sansanonin Amurka da ke fadin yankin.
IRGC ta ce za a ci gaba da kai munanan hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan wuraren taron sojojin Isra'ila a Arewa da kuma yankin Gaza.
Asali: Legit.ng
