An Fitar da Bidiyon Yadda Rokokin Iran Suka Ruguza Isra'ila

An Fitar da Bidiyon Yadda Rokokin Iran Suka Ruguza Isra'ila

  • Rahotanni sun nuna cewa Iran ta kaddamar da wasu munanan hare-hare a babban birnin Isra'ila, Tel Avid a yau Talata, 24 ga Maris, 2026
  • Kafar yada labaran Isra'ila ta tabbatar da rugujewar gine-gine masu tarin yawa da jikkata wasu 'yan kasar a jerin hare-haren da aka kai
  • An fitar da wani bidiyon da aka dauka da jirgi maras matuki da ya nuna irin barnar da aka yi a Isra'ila, inda jama'a ke tofa albarkacin bakinsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Irsa'ila - Kasar Isra'ila na cigaba da fuskantar manyan hare-haren da ke jawo rushewar gine-gine da jikkata mutane daga dakarun Iran.

Sojojin Iran sun kara kaimi wajen kai hari ne a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump ya fara maganar tsagaita wuta bayan shiga mako na uku da yakin.

Kara karanta wannan

Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya

Wajen da Iran ta rusa a Isra'ila
Wasu gine-gine da Iran ta ruguza a Tel Aviv, Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta wallafa bidiyon yadda hare-haren Iran suka ruguza wani sashe na babban birnin kasar Isra'ila a shafinta na X.

Bidiyon ruguza babban birnin Isra'ila

Bidiyon da aka dauka da jirgi maras matuki ya nuna mummunar lalacewa da ta samu wani gini mai hawa da yawa a birnin Tel Aviv, bayan jerin hare-haren makaman roka da Iran ta kai Isra’ila.

Ga bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan rusau a Isra'ila

Wani mai amfani da X, @LOTAMOSANA, ya ce:

“Idan ba a dakatar da wannan ba yanzu, Isra’ila za ta lalace fiye da Gaza.”

Samsul Haque ya ce:

“Har yanzu bai kai abin da ya faru a birnin Gaza ba.”

Samuel Osei kuwa cewa ya yi:

“Na ji dadin yadda Isra'ila ta zama sabuwar Gaza.”

Shafin 247 Update ya yi tambaya da cewa:

“Girman barnar da aka nuna a nan yana da yawa. Shin akwai rahotannin adadin wadanda suka jikkata ko suka mutu a hukumance?”

Kara karanta wannan

Iran ta ƙaddamar da harin makami mai linzami kan cibiyar haɗa nukiliyar Isra'ila

AA Pakistan ya ce:

“Ana kai hari kan fararen hula adukkan bangarorin biyu, dole ne a dakatar da yakin kafin a sake rasa rayuka.”

Iran ta jikkata mutane a Isra'ila

Wani harin roka daga Iran ya jikkata mutane hudu tare da lalata kadarori sosai a Tel Aviv da safiyar Talata, bayan da Isra’ila ta kai hare-haren sama kan wurare da dama na gwamnatin Iran a daren da ya gabata.

Harin na daga cikin jerin hare-haren da Iran ta kai cikin dare daga Litinin zuwa safiyar Talata, inda aka kai hare-hare a Arewa, Kudu da Tsakiyar Isra’ila, wanda ya sa dubban mutane suka rika gudu zuwa mafaka don tsira.

Benjamin Netanyahu a wajen da Iran ta kai hari
Firaminista Netanyahu a wajen da Iran ta kaiwa Hari a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Times of Israel ya ce a Tel Aviv, jami’an lafiya sun ce sun yi wa mutane hudu magani a wurin da rokar da Iran ta harba ta fado.

Iran ta nuna rumbun makamai

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Iran ta wallafa wani bidiyo da ke nuna wani rumbun makamai a karkashin kasa.

Kara karanta wannan

Ana cikin murnar Sallah, Iran ta shammaci Amurka da Isra'ila a sababbin hare hare

Hakan na zuwa ne bayan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa kasar, lamarin da ke nuna cewa a shirye take da cigaba da yaki.

A cikin bidiyon da Iran ta fitar, an nuna wani waje da ke dauke da tarin makamai masu linzami da manyan motocin yaki da ake amfani da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng